Madalla! Malamin da aka sace a jami'ar Patakwal ya kuɓuta

Madalla! Malamin da aka sace a jami'ar Patakwal ya kuɓuta

- Wani malami da aka sace sama da sati uku da suka gabata a jami'ar Patakwal (UNIPORT) ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane.

- Dr. Jones Gilbert Ayuwo, malami ne dake koyar wa a tsangayar koyarda harsuna da sadarwa na jami'ar ta Patakwal

- Rahoto ya bayyana cewa yanzun haka malamin na gidan kwanan malamai dake jami'ar Patakwal.

Wani malami dake koyarwa a jami'ar Patakwal, jihar Rivers mai suna Dr. Jones Gilbert Ayuwo ya samu kuɓuta daga hannun mutanen da suka yi garkuwa dashi bayan kimanin sati uku a hannun su.

KARANTA ANAN: Ba wani abu dake aiki a Najeriya, Wani jigon PDP ya caccaki gwamnatin APC

Rahotanni sun bayyana cewa an saki malamin ne da sanyin safiyar yau Talata, sai dai har yanzun babu cikakken bayanin yadda ya samu kuɓuta daga hannun waɗanda suka yi garkuwa dashi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, an kira mai magana da yawun 'yan sandan jihar ta Rivers lokuta da dama domin jin ta bakin sa akan sakin malamin amma bai ɗaga wayar ba.

Madalla! Malamin da aka sace a jami'ar Patakwal ya kuɓuta
Madalla! Malamin da aka sace a jami'ar Patakwal ya kuɓuta Hoto: @uniport
Asali: Twitter

Sai dai da yawa daga cikin kafafen watsa labari dake Patakwal ɗin sun bayyana kubutar nalamin jami'ar a shirye-shiryen su na yau.

kARANTA ANAN: Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani A Gaban Kotu Kan Tuhumar Zamba Cikin Aminci

Yanzu haka malamin na gidan kwanan malamai dake cikin makarantar UNIPORT.

Dr. Jones Gilbert Ayuwo sanannen mutum ne a garin Andoni, an sace shi a ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu a hanyar Ogoni zuwa Andoni.

An yi gaba da malamin ne lokacin da yake hanyarsa ta dawo wa daga wani taro daya halarta na fassara littafin Bible daga harshen turanci zuwa harshen Andoni.

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kudade Ga Wadanda Rikicin Boko Haram Da Annobar Korona Ya Shafa A Yobe.

Ministar ma'aikatar jinkai, Sadiya Farouk ce ta ƙaddamar da shirin a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe.

Ministar ta bayyana cewa za'a raba N20,000 ga mutane kimanin 10,000 da lamarin ya shafa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262