Gwamnatin Tarayya Ta Raba Kudade Ga Wadanda Rikicin Boko Haram Da Annobar Korona Ya Shafa A Yobe
- Gwamnatin tarayya ta fara raba kuɗaɗe ga talakawan da annobar cutar korona da kuma rikicin Boko Haram ya shafa a jihar Yobe
- Ministar ma'aikatar jinkai, Sadiya Farouk ce ta ƙaddamar da shirin a Damaturu, babban birnin jihar ta Yobe
- Ministar ta bayyana cewa za'a raba N20,000 ga mutane kimanin 10,000 da lamarin ya shafa
Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin kudi ga talakawa da gajiyayyun mata wadanda rikicin Boko Haram da annobar korona ya ritsa da su a jihar Yobe.
Ministar ma'aikatar jin ƙai, Sadiya Farouk, a yayin ƙaddamar da shirin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, tace burin tallafin shine samar da wadataccen jari ga matan domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.
KARANTA ANAN: Covid-19: NAFDAC tayi kakkausan gargaɗi a kan allurar rigakafin bogi
Ta ce gwamnatin jihar Yobe ta amshi kudi fiye da 980 miliyan karkashin shirin gwamnatin tarayya na raba kudade tun daga fara shi.
Kimanin kananan hukumomi 6 ne ke cin gajiyar shirin a jihar ta Yobe, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari
Ta yi bayanin cewa za'a raba dubu 20 ga kimanin mutane dubu 10 domin rage raɗaɗin annobar cutar korona.
An kirkiro shirin tallafin kudin ne a karkashin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari domin rage raɗaɗin talauci.
A wani labarin kuma Rundunar 'yan sanda sun cafke mutane 101 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka
Daga cikin laifuffukan da ake zargin mutanen da aikatawa akwai; garkuwa da mutane, satar ababen hawa da kuma shaye-shaye.
'Yan sandan sun sami wannan gagarumar nasarar ne tun bayan kama aikin sabon kwamishinan 'yan sandan jihar, Sama’ila Shu’aibu Dikko.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng