Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani A Gaban Kotu Kan Tuhumar Zamba Cikin Aminci

Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani A Gaban Kotu Kan Tuhumar Zamba Cikin Aminci

- Hukumar ƴan sanda ta gurfanar da wani matashi mai sana'ar fenti a gaban kotu kan laifin ha'intar kwastomansa wasu kuɗaɗe.

- Ana zargin matashin ɗan kimanin shekara 35 mai suna Aliyu Abubakar da yaudarar kuɗi 1.3 miliyan.

- Mai ƙarar yace ya bawa Aliyu kuɗi ne da niyyar ya siyo mishi riɗi amma sai ya cinye kuɗin.

An gurfanar da, Aliyu Abubakar, mai sana'ar fenti ɗan kimanin shekaru 35 a gaban kotun hukunta manyan laifuka dake wuse zone 6 Abuja bisa tuhumar sa da laifin damfara ta kuɗi 1.3 miliyan.

Yan sanda sun tuhumi Aliyu Abubakar wanda ke zaune a garin Abaji da laifin cin amana da kuma ha'inci, Leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Buhari, Atiku, PDP da APC sun taya Wiz Kid da Burna Boy lashe kyaututtukan waka

Jami'i mai tuhuma, Kufreabasi Ebong, ya shaida ma kotu cewa, a ranar 5 ga watan Maris ɗin nan ne dai Saleh Mustapha ya kawo ƙarar Aliyu ga kwamishnan ƴan sanda na yankin birnin tarayya.

Ebong ya ƙara da cewa, mai ƙarar yace ya bama wanda ake tuhuma kuɗi har 1.3 miliyan da zummar ya siyo mishi riɗi.

Yace amma maimakon haka, sai kawai ya cigaba da hidin-dimun shi da ƙuɗin ba tare da wani bayani ba.

Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani A Gaban Kotu Kan Tuhumar Zamba Cikin Aminci
Yan Sanda Sun Gurfanar Da Wani A Gaban Kotu Kan Tuhumar Zamba Cikin Aminci Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kwamitin tuhumar yace wannan laifi dai da ya aikata ya saɓa ma sashe na 312 da kuma na 322 na kundin laifuka da hukunce-hukuncensu.

KARANTA ANAN: Rundunar 'yan sanda sun cafke mutane 101 da ake zargi da aikata manyan laifuffuka

Duk da dai kotu bata samu wanda ake tuhuma da laifi ba.

Alkaliyar dake shari'ar Linda Chidinma ta bayar da wanda ake tuhuma beli akan N400,000 tare da sharaɗin cewa zai kawo mutum ɗaya da zai tsaya mishi.

Tace dole ne wanda zai tsaya mishi ya kasance ma'akaicin gwamnatin tarayya da yakai aƙalla mataki na 08 ko sama da haka, ko kuma ya kasance yana aiki da wata sananniyar ma'aikata a cikin Abuja.

Ta ƙara da cewa dole ne ya kasance kotun ta tabbatar da inganci gami da cikar sharuɗɗan. Sannan alƙaliyar ta ɗaga zaman kotun sai zuwa 21 ga watan Aprilu me zuwa.

A wani labarin kuma Farashin wasu kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan

Rahotanni daga hukumar dillancin labarai na kasa watau NAN su na zuwa cewa farashin kayan gwari da ganye sun yi kasa a kasuwannin jihar Kano.

Darajar kayan miya da ganye da sauran makusanta kasa ya fadi yanzu da sama da 200% a kasuwannin Kofar Wambai da na Rimi a cikin garin Kano.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban- daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Source: Legit Newspaper

Online view pixel