Ba wani abu dake aiki a Najeriya, Wani jigon PDP ya caccaki gwamnatin APC

Ba wani abu dake aiki a Najeriya, Wani jigon PDP ya caccaki gwamnatin APC

- Wani jigo a jam'iyyar hamayya ta PDP ya caccaki gwamnatin APC ƙarkashin jagorancin shugaba Buhari

- Sanata Samuel Anyanwu yace jam'iyya mai mulki ta gaza cika alƙawurran data ɗaukar ma 'yan Najeriya

- Yace maimakon gyara da tace zata yi, APC ta ƙara ruguza ƙasar domin babu wani abu dake aiki

Jigo a jam'iyyar PDP, sanata Samuel Anyanwu, ya koka kan yadda jam'iyya mai mulki APC ta ba yan Najeriya kunya wajen kin cika alkawuran da ta dauka.

A lokacin da yake magana a Owerri, Anyanwu, ya koka kan yadda matsalar rashin tsaro a kasa, karuwar talauci da rashin aikin yi ya saka mutane cikin halin kunci da ƙaƙa ni kayi.

KARANTA ANAN: Farashin wasu kayan abinci sun fadi war-was a Kano ana daf da fara azumin Ramadan

A cewar tsohon sanatan:

"APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari sun tabbatar wa da yan Najeriya zasu tsamo su daga yanayin rayuwa, gina tituna masu kyau, bada ilmi mai inganci da bunkasa noma"

"Yau dukkanin alkawuran su ya zama yaudara ne domin sun amshi mulki amma har yanzin 'yan Najeriya ba suga komai ba. Yanzu an tagayyara yan Najeriya sannan kuma an kyalesu." inji shi.

Ba wani abu dake aiki a Najeriya, Wani jigon PDP ya caccaki gwamnatin APC
Ba wani abu dake aiki a Najeriya, Wani jigon PDP ya caccaki gwamnatin APC Hoto: @sen_anyanwu
Source: Twitter

KARANTA ANAN: Atiku ya sake jan hankalin gwamnatin Buhari biyo bayan sace dalibai a Kaduna

Ya Ƙara da cewa: "Babu wani abu da yake aiki a kasar nan, ko mutane da dukiyoyin su ba'a bari ba. Abin takaici kasar da take da albarkatun kasa tana kara kudin mai yadda taso. "

"Ba abinda yake daidai, kudin kayan masarufi suna ta hauhawa kuma basu dawowa," a cewarsa

"Babu mai barci cikin natsuwa. Al'umma sun firgita da shirin halin ko ta kwana a ko yaushe. Maaikatan gwamnati da yan fansho da mutane na kuka"

"Har yanzu anki biyan maaikata da yan fansho. Yunwa tana ta dada karuwa" inji shi

PM News ta ruwaito.

A wani labarin kuma Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Najeriya

Kamar yadda Sheikh Mahi Nyass ya sanar, ana nadi ne bayan malamai sun tantance mutum kuma Khalifatul Arrm ya bashi takardar shaida.

A cewar Sheikh Mahi, Tsohon sarkin Kano bai nuna bukatar kujerar ba balle a kai ga tantancesa har ayi masa nadin.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban- daban.

Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77

Source: Legit.ng

Online view pixel