2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa

2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na fuskantar kalubale game da kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa

- Wata kotun Abuja ce za ta yanke hukunci idan dan siyasar zai iya tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya nan gaba

- Atiku ya kasance dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2019

Za a iya hana tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar tsayawa takarar shugaban kasa idan har karar da ke neman a hana shi tayi nasara a kotu.

Sai dai dan siyasar ya nemi babbar kotun tarayya ta Abuja da ta yi watsi da karar wacce ke neman hana shi tsayawa takarar shugaban kasa a nan gaba.

KU KARANTA KUMA: Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye

2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa
2023: Rashin tabbas yayin da Atiku ke fuskantar yiwuwar hana shi takarar neman kujerar shugaban kasa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa shari’ar da ke kalubalantar cancantar Atiku na tsayawa takarar shugaban kasa wata kungiya ce ta shigar da ita a karkashin inuwar Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa.

Mai shigar da karar ya yi korafin cewa Atiku ba dan Najeriya bane ta asali kuma don haka bai cancanci tsayawa takarar zama shugaban kasar Najeriya ba.

KU KARANTA KUMA: Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan

Kungiyar ta bayyana cewa la’akari da yanayin da ke tattare da haihuwar Atiku, an haife shi ne a Arewacin Kamaru a shekarar 1957 kafin raba gardamar da aka yi a ranar 1 ga Yuni, 1961, wanda ya sanya Arewacin Kamaru ta zama wani bangare na Najeriya.

Mai shigar da karar ya ce wannan yana nufin cewa Atiku ba dan Najeriya bane ta asali.

Amma a cikin takardar da wani Nanchang Ndam ya gabatar a madadinsa, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya kamata a yi watsi da karar da ke kalubalantar cancantarsa gaba daya.

A karar da aka shigar mai lamba FHC / ABJ / CS / 177, Atiku da sauran wadanda ake kara ciki har da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta(INEC), da kuma atoni janar na tarayya sun ce karar ba ta da inganci.

A matakin farko na kin yarda da korafin cikin hadin gwiwa da PDP, Atiku ya jaddada cewa shi dan asalin Tarayyar Najeriya ne.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Mayu, tana mai jaddada cewa za a saurari karar tare da adawa ta farko ta Atiku. Ya ba da umarnin yin sanarwar ji a dukkan bangarorin.

A wani labarin, Ministan yada labarai da al'adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed yayi martani ga shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo.

Kamar yadda ministan Buhari ya sanar, gwamnatin nan bata da lokacin batawa a kan mai neman suna da nishadantar da jama'a.

Asari Dokubo, shugaban tsagerun yankin Neja Delta, ya bayyana cewa ya kafa gwamnatin gargajiya ta Biafra kuma shine shugaba.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel