Ba a turawa Shehu Sani kudi a asusunsa ba – Shaidawa sun fadawa kotu

Ba a turawa Shehu Sani kudi a asusunsa ba – Shaidawa sun fadawa kotu

Wasu ma’aikatan banki sun bada shaida a shari’ar da ake yi tsakanin Sanata Shehu Sani, da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa.

Beckley Ojo da Elizabeth Nwoka da ke aiki da wani babban banki da ke Najeriya sun bayyana abin da su ka sani ne a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja a Ranar Laraba.

Ma’aikatan bankin sun tsaya a matsayin shaidu na hukumar EFCC a kan tsohon Sanatan jihar Kaduna ta tsakiya, Kwamred Sani, a gaban Alkali mai shari’a, Inyang Ekwo.

Kamar yadda mu ka samu labari, shaidun sun gabatar da wasu takardun banki da ke nuna yadda aka tura kudi a cikin asusun bankin wasu mutane daga kamfanin motocin ASD.

Lauyan da ke kare EFCC, Abba Mohammed, shi ne ya gabatar da Ojo da Muka a matsayin shaidunsa na farko. Sai dai ba su iya nuna cewa kamfanin ya turawa Sani kudi ba.

KU KARANTA: Bayelsa: An yi fatali da karar Jam'iyyar APC a kotun koli

Ba a turawa Shehu Sani kudi a asusunsa ba – Shaidawa sun fadawa kotu
Ana zargin Sanata Shehu Sani da cin kudin kamfanin ASD
Asali: UGC

Shaidan farko da aka kira ya fadawa Alkali cewa Kamfanin ASD sun turawa wani ‘Dan kasuwa Sheriff Shanono kudi har Naira miliyan uku zuwa asusunsa a shekarar bara.

Fitaccen ‘Dan kasuwan na jihar Kaduna, Alhaji Sani Dauda, shi ne mai kamfanin ASD. Sani Dauda ya na tuhumar Shehu Sani da karbar kudi har fam $25, 000 daga hannunsa.

An gabatar da takardun bankin kamfanin motocin a matsayin hujjoji a kotu. Da ta ke magana, Elizabeth Nwoka ta fadawa kotu cewa ta yi shekaru takwas ta na aiki da bankin.

Abdul Ibrahim shi ne Lauyan da ke kare Shehu Sani a kotu. Ibrahim ya tambayi shaidan ko Sanatan ya na cikin wadanda aka turawa kudi, shaidan ya nuna bai da tabbas.

Bayan sauraron maganganun da shaidun su ka yi, Alkalin ya dage shari’ar zuwa Ranar Laraba. Ana sa ran hukumar EFCC za ta cigaba da kiran shaidun da za su tsaya mata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel