Shehu Sani ya maka EFCC a kotu, ya bukaci wasu makuden kudin diyya

Shehu Sani ya maka EFCC a kotu, ya bukaci wasu makuden kudin diyya

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya maka hukumar yaki da rashawa ta EFCC a kotu saboda tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba na kusan makonni uku.

Lauyan Shehu Sani, Abdul Ibrahim ya bayyana cewa sun mika karar gaban mai Shari'a A. B. Mohammed na babban kotun tarayya dake Gudu a Abuja. Za a fara sauraron karar a ranar Litinin 20 ga watan Janairu na 2020.

Ibrahim ya shigar da karar ne ta bukatar bin hakkin tsohon Sanatan da EFCC da mamallakin ASD Motors. Lauyan ya bayyana cewa wanda yake karewan na bukatar naira miliyan dari ne daga hukumar yaki da rashawa ta EFCC din.

Idan zamu tuna, a halin yanzu tsohon sanatan na hannun EFCC a kan zarginsa da ake da karbar $25,000 daga mai ASD Motors, Alhaji Sani Dauda, tare da alkawarin zai mika kudin ga mukaddashin shugana EFCC, Ibrahim Magu.

DUBA WANNAN: Ku dena kiran mu NEPA idan kuna son wutan lantarki - DisCos

Idan zamu tuna, Suleiman Ahmed, wanda ya na cikin Hadiman tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya watau Shehu Sani, ya fayyace shari’ar da ake yi tsakanin Mai gidan na sa da hukumar EFCC a wata hira. Ahmed ya ce Shehu Sani ya fara haduwa da Sani Dauda ne bayan da ya samu sabani da wani Surukinsa har aka tsare sa, a dalilin haka Sanatan ya je gida domin ya yi masa jajen lamarin.

Wajen wannan ziyara ne shugaban kamfanin na ASD Motors ya yi wa Sani tallar wata mota. A karshe Sani Dauda ya yi masa alfarma ya biya kudin motar gutsun-gutsun inji Hadiminsa.

“Wata rana ya kai masa ziyara a ofis a Kaduna ya ba shi $13000, daga baya ya kara masa $11000. Daga nan ya ba shi takardar shaida da lambar banki domin ya tura ragowar kudin motar.”

A game da shiga hannun EFCC, Ahmed ya ce a Ranar karshe ta 2019 EFCC ta gayyaci Sanatan ya zo ofishinta, kuma ya je salin-alin, a nan aka soma zarginsa da cewa Dauda ya ba shi wasu kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: