Magu: An samu wasu Miyagu su na cin karensu babu babbaka a EFCC- Sani

Magu: An samu wasu Miyagu su na cin karensu babu babbaka a EFCC- Sani

A daidai lokacin da tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya ke tsare, bayanai sun fara fitowa a game da irin rikon da ya yi a lokacin da ya ke kan kujera.

Shehu Sani ya bayyana cewa Ibrahim Magu wanda wasu ke ganin cewa ta shi ta zo a karshe a yanzu, ya rika amfani da wasu miyagu da ake kira ‘Yaran Magu’ a lokacin da ya ke kan kujera.

Tsohon sanatan ya ce jami'an da ke cikin wannan gungu na ‘Yaran Magu’ ko yaran oga da aka kafa shekarun baya, duk sun fito ne daga wani bangare guda na kasar nan.

Ibrahim Magu mai shekaru 58 a Duniya asalinsa mutumin garin Maiduguri ne a jihar Borno. Ya na cikin wadanda su ka taimakawa Nuhu Ribadu a lokacin da ya ke rike da EFCC.

Sanata Shehu Sani ko da ba a ji mutuwar sarki a bakinsa ba, ya nuna cewa sauran ma’aikatan EFCC su na da labarin aikin da wadannan yara da Magu ya kafa su ka rika yi.

“Abin da za ka yi kurum shi ne ka tambayi sauran jami’an hukumar masu gaskiya su fada maka abin da su ke yi.” Sani ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

KU KARANTA: An bude sabon babi a binciken da ake yi a kan Magu

Ibrahim Magu: An samu wasu Miyagu su na cin karensu babu babbaka a EFCC- Sani
Ibrahim Magu Hoto: Twitter/EFCC
Asali: UGC

Ba Sani kadai ya ke zargin Ibrahim Magu da ba daidai wajen aiki ba. Olusegun Adeniyi wanda ya yi aiki da tsohon shugaban kasa Ummaru ‘Yar’adua bai yi kalamai masu dadi game da Magu ba.

Olusegun Adeniyi ya ce tsohon shugaban hukumar ta EFCC ya rika wulakanta wasu manya da ake ji da su a kasar nan a lokacin da ya ke ofis, daga cikinsu har da tsohon shugaban kasa.

A rahoton da DSS ta fitar game da Magu a 2016, ta zarge shi da yin karfa-karfa kamar ana mulkin soji. Ana kuma zargin cewa shi kan sa mukaddashin shugaban na EFCC ya na da kashi a gindi.

Hukumar DSS ta ce Magu ya na aiki ne da jita-jita, malaman tsibbu, tare da kuma shigar da siyasa wajen aikinsa. A dalilin wannan majalisa ta ki tantance shi har sau biyu.

A baya an zargi Magu da rashin sanin kan aiki, da cin mutuncin hukumomi ma’aikatun gwamnati domin wata manufarsa, wanda hakan ya batawa EFCC suna a idon Duniya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng