Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Jihar Abia da Akwa Ibom, Mutum ɗaya ya rasa ransa

Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Jihar Abia da Akwa Ibom, Mutum ɗaya ya rasa ransa

- Rikici ya ɓarke tsakanin mazauna wasu garuruwa biyu daga jihohin Abia da Akwa Ibom har yakai ga kashe mutum ɗaya

- Rikicin ya ɓarke ne tsakanin jama'ar garin Ugbo dake karamar hukumar Arochukwu jihar Abia da na Ikpanja karamar hukumar Ibiono, jihar Akwa Ibom

- Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin amma sun ce an ɗauki matakin gaggawa a jihohin biyu, kuma ƙura ta fara lafawa

Mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa kuma an sace 15 bayan rikici ya ɓarke tsakanin ƙaɓilu guda biyu a jihohin Abia da Akwa Ibom.

Rikicin ya ɓarke ne tsakanin mazauna garin Ugbo dake karamar hukumar Arochukwu, a jihar Abia, da kuma jama'ar dake zaune a Ikpanja, karamar hukumar Ibiono Ibom a jihar Akwa Ibom.

KARANTA ANAN: Kyakyawar budurwa da kawayenta 5 sun zama likitoci, hotonsu ya gigita jama'a

Mazauna garin Ugbo sun yi kira ga gwamnatin jihar Abia da ta kawo musu ɗauki don gudun ƙara rasa rayukan al'ummar su.

Wani shugaba a garin, Mazi Jerry Onwumere, yace za'a iya samun ƙarin rasa rayuka da dama matuƙar gwamnati ba ta ɗau matakin daƙile lamarin ba.

Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Jihar Abia da Akwa Ibom, Mutun ɗaya ya rasa ransa
Rikicin ƙabilanci ya ɓarke a Jihar Abia da Akwa Ibom, Mutun ɗaya ya rasa ransa Hoto: @aksgovt
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Hukumar EFCC ta koma Kotu da Shehu Sani, an saurari hujjar wayar da aka yi da Sanatan

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Abia, Chief John Okiyi- Kalu, ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro yankin da ake rikicin, Punch ta ruwaito

Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sanda, Geoffrey Ogbonna, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Yace an tsinci gawar mutum ɗaya wanda aka kashe kuma aka cire masa kai, an kai gawar mutuware.

Ya ƙara da cewa, jami'an 'yan sanda daga jihohin biyu sun isa yankunan da abun ya shafa don dakile lamarin, kuma ƙura ta fara lafawa a garuruwan.

A wani labarin kuma FG tayi martani ga ikirarin Asari Dokubo na kafa sabuwar gwamnatin Biafra.

Ministan yada labarai da al'adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed yayi martani ga shugaban tsagerun Neja Delta , Asari Dokubo.

Kamar yadda ministan Buhari ya sanar, gwamnatin nan bata da lokacin batawa a kan mai neman suna da nishadantar da jama'a.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano. Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel