FG tayi martani ga ikirarin Asari Dokubo na kafa sabuwar gwamnatin Biafra
- Ministan yada labarai da al'adun Najeriya, Alhaji Lai Mohammed yayi martani ga shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo
- Kamar yadda ministan Buhari ya sanar, gwamnatin nan bata da lokacin batawa a kan mai neman suna da nishadantar da jama'a
- Asari Dokubo, shugaban tsagerun yankin Neja Delta, ya bayyana cewa ya kafa gwamnatin gargajiya ta Biafra kuma shine shugaba
Gwamnatin tarayya ta kwatanta rahoton samar da gwamnatin gargajiya ta Biafra da Asari Dokubo yayi da wasan yara daga mutum mai bukatar jan hankalin jama'a.
A yayin jawabi ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a kan wannan cigaba a Legas ranar Litinin, ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, yace hankalin shugaban kasa ba zai dauku da wannan shirmen ba.
"Idan Asari Dokubo na son kafa gwamnatin gwaji ne, zai iya yin hakan. Hankalin wannan gwamnatin ba zai dauko da shirmensa ba saboda muna da abubuwan yi.
KU KARANTA: Darikar Tijjaniya ta musanta baiwa Muhammadu Sanusi II shugabanta na Najeriya
"Ba mu da lokacin saurare ko batawa a kan ire-iren Dokubo wanda ke neman suna kawai.
“Za mu dauka zantukansa a matsayin daya daga cikin wasan nishadi. Wani abun dadi shine ba a taba zama a Najeriya babu nishadi," yace.
KU KARANTA: NYSC ta saki jerin sunayen jami'o'i 8 da ta hana dalibanta hidimar kasa a Najeriya
A wani labari na daban, Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya ja kunnen Bello Matawalle a kan siyasantar da kalubalen tsaro da ke addabar jihar.
A yayin jawabi ga manema Labarai a ranar Litinin a Talatan Mafara, Yari ya shawarci Matawalle da "yayi tunani mai zurfi a kan kowacce shawara da aka bashi wurin shawo kan matsalar tsaro."
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya bukaci Matawalle da ya hada kai da gwamnatin tarayya wurin shawo kan matsalar.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng