Yan bindiga sun saki bidiyon daliban Kaduna 39 da suka sace, sun bukaci N500m, sun bada lambar kiransu

Yan bindiga sun saki bidiyon daliban Kaduna 39 da suka sace, sun bukaci N500m, sun bada lambar kiransu

- Bayan kwana daya hannun yan bindiga, an ga fuskokin mutane 39 da aka sace a jihar Kaduna

- Yan bindiga sun afka cikin makarantarsu dake Afaka cikin dare suka yi awon gaba da su

- Yanzu yan bindigan na bukatan rabin biliyan matsayin kudin fansa

Yan bindigan da suka sace daliban makarantar FCFM Afaka a jihar Kaduna sun bukaci N500m daga wajen gwamnatin jihar domin fansan dalibai 39 - Mata 23 da Maza 16.

Daily Trust ta rahoto cewa akalla iyayen uku cikin daliban sun tabbatar da cewa yan bindigan sun tuntubesu kuma sun bukaci N500m kafin su sakesu.

Hakazalika yan bindigan sun saki bidiyoyi uku na daliban da suka sace cikin daji.

Har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba tayi jawabi kan bidiyoyin ba kuma kwamishanan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya ki amsa wayansa yayinda aka tuntubesa.

Amma, gwamnan Nasir El-Rufa'i a hirar da yayi a tashar Channels ya ce bai zai yi sulhu da yan bindigan ba kuma ba zai biya kudin fansa ba.

Yan bindigan sun yi amfani da shafukan Facebook na daliban wajen sakin bidiyon.

DUBA NAN: Mun nemi kudin makaman da muka baiwa su Buratai mun rasa, NSA Monguno yayi fallasa

Yan bindiga sun saki bidiyon daliban Kaduna 39 da suka sace, sun bukaci N500m, sun bada lambar kiransu
Yan bindiga sun saki bidiyon daliban Kaduna 39 da suka sace, sun bukaci N500m, sun bada lambar kiransu
Asali: Twitter

DUBA NAN: Kudin makamai: Monguno ya gyara zancensa, ya ce tsofaffin hafsoshi ba su yi sata ba

A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda yan bindiga suka zagayesu sanye da kayan Sojoji suna zanesu.

A cikin bidiyon da aka saki misalin karfe 12:00 na ranar Asabar ta manhajar Facebook na Tasha Sandra, ana iya ganin daliban cikin daji tare da yan bindigan suna dukansu.

Tasha Sandra tace: "Wannan ba bidiyon bogi bane. Ku taimakemu ku biya kudin da suke bukata kuma kada kuyi kokarin turo Sojoji ceto mu saboda zasu kashemu."

"Ina kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha su kawo kudin fansa N500 million. Ga lamba daya tilo da za'a iya samunsu 09023404650."

Daya daga cikin daliban yace: "Suna na Abubakar Yakubu. Dalibin kwalejin gwamnatin tarayya na ilmin gandun daji Kaduna. Ina kira ga gwamnan jihar Kaduna, gwamnatin jihar Kaduna da gwamnatin tarayya."

Jiya mun kawo muku cewa jami'an tsaro sun ceto dalibai kimanin 180 a cikin wadanda aka sace a kwalejin zamanantar da gandun daji dake Afaka, unguwar Mando ta jihar Kaduna.

Kwamishanan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya bayyana hakan inda yace ana kokarin ceto sauran.

Aruwan ya bayyana yadda yan bindigan suka kutsa cikin makarantan cikin dare sukayi awon gaba da daliban.

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Asali: Legit.ng

Online view pixel