Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari

Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari

- Sanata Shehu Sani yayi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba'a kan yadda yake jan kunnen 'yan bindiga

- Ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dinga jan kunnen 'yan bindiga da yaren da suke ji ba Turanci ba

- Ya yi wannan tsokacin ne sakamakon satar 'yan makaranta da 'yan bindiga suke yi a jihohin kasar nan

Shehu Sani, tsohon sanatan Najeriya ya yi tsokaci ga shugaban kasa Muahmmadu Buhari a kan yadda 'yan bindiga ke yawan kai hare-hare.

Sau da yawa bayan hare-haren, shugaban kasa na yin jan kunne ga 'yan bindigan ta bakin hadiminsa, Malam Garba Shehu.

Bayan sace yaran makarantar Jangebe dake jihar Zamfara, shugaban kasa yace 'yan bindigan basu fi karfin gwamnatinsa ba.

KU KARANTA: Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno

Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari
Ka daina jan kunnen 'yan bindiga da Turanci, kayi da yarensu, Shehu Sani ga Buhari. Hoto daga @Thacableng
Asali: UGC

Yana jan kunnensu da su daina kai hare-haren ko kuma ya murkushesu.

Amma a makonnin da suka gabata bayan harin da suka kai, gwamnatin tarayya tace harin Jangebe ne zai kasance na karshe da 'yan bindiga za su kwashe daliban Najeriya.

A makon da ya gabata sai ga wasu 'yan bindiga sun kai hari Kwalejin horar da aikin noma da gandun dabbobi dake Afaka a jihar kaduna.

Bayan nan, shugaban kasa ya bada sabon jan kunne inda yake cewa ba zai bar harkar ilimi ta tabarbare ba a kasar nan.

Amma a tsokacin da yayi kama da ba'a, Sani ya bukaci fadar shugaban kasa da ta dinga bada jan kunnen a yaren da 'yan bindigan suke ji ba Turanci ba.

"Dukkan jan kunne da za a yi wa 'yan bindiga kamata yayi a dinga yin shi a yaren da suke ji kuma zasu gane. Jan kunnensu a Turanci bashi da amfani," ya wallafa.

KU KARANTA: Rikicin manoma da makiyaya: Ka gaggauta yin taron tsaron kasa, Tinubu ga Buhari

A wani labari na daban, Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai ga gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ruda 'yan bindiga da 'yan ta'adda a kasar nan da wa'adin da yake basu tare da jan kunne.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama a watan da ya gabata saboda kalubalantar mulkin Buhari da jam'iyyarsa ta APC, ya sanar da hakan ne a ranar Asabar.

A ranar Juma'a ne jaridar Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka kutsa kwalejin harkar noma da gandun dabbobi dake Kaduna suka kwashe dalibai.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng