Rikicin manoma da makiyaya: Ka gaggauta yin taron tsaron kasa, Tinubu ga Buhari
- Jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya bukaci Buhari ya tara taron masu ruwa da tsaki a kasar nan
- Ya ce akwai bukatar shugaban kasan ya shawo kan matsalar manoma da makiyaya a kasar nan
- Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne, yace inganta tsaro zai zama hanyar kawo karshen rikicin
Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta tara taron masu ruwa da tsaki wurin shawo kan matsalar rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar nan.
A makonni kadan da suka gabata ne aka dinga rikici a kan zargin da ake wa makiyaya da kashe-kashe tare da garkuwa da mutane a kudu maso yammacin kasar nan.
A watan Janairun da ta gabata ne Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bukaci makiyaya da su bar dukkan dajikan jiharsa.
Jaridar The cable ta ruwaito cewa, Sunday Igboho, matashi mai rajin kare hakkin Yarabawa ya bukaci makiyayan da su bar karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo.
KU KARANTA: Ganawar Gumi da 'yan bindiga: Sun sha alwashin addabar El-Rufai da jihar Kaduna
A kokarin shawo kan matsalar, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa jami'an tsaro umarnin harbe duk wanda aka kama da AK-47 ba bisa ka'ida ba.
A wata takarda da ya fitar ranar Asabar, shugaban jam'iyyar APC yace manoma da makiyaya na bukatar tallafi domin inganta yadda suke tafiyar da al'amuransu.
Ya ce hukumomin tsaro da tabbatar da an bi doka ake bukata a karkara kuma akwai bukatar gwamnatocin tarayya da na jihohi su samar da sabbin hanyoyin fasaha na inganta tsaro.
Tsohon gwamnan yayi kira a kan cewa a yi taron masu ruwa da tsaki domin shawo kan matsalar tsaro kuma a samar da hanyar kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.
KU KARANTA: Yadda Ironsi, Gowon, Obasanjo suka dasa tubalin rashin tsaro a Najeriya, Sarkin Musulmi
A wani labari na daban, ragowar daliban kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Afaka a Mando, jihar Kaduna an kwashesu zuwa barikin Div 1 Garrison Command a Kaduna.
Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga makarantar inda suka kwashe dalibai mata.
Wata majiya daga rundunar soji ta sanar da Daily Trust cewa ba don kokarin jami'an rundunar sojin sama ba da na Div 1 dake Kaduna, da harin sai ya fi haka kazanta.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng