Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno

Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno

- Hukumar EFCC tace bata da tabbacin za ta binciki tsoffin shugabannin tsaron da suka gabata

- Wannan ya biyo bayan ikirarin da NSA Monguno yayi na cewa wasu kudaden makamai sun yi batan dabo

- EFCC ta sanar da cewa bata da wata shaida da aka gabatar a gabanta mai nuna cewa an kwashe kudin makaman

Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta magantu a kan fallasar da Manjo Janar Babagana Monguno yayi na cewa makuden kudade na siyan makamai sun bace.

Monguno ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da BBC Hausa a ranar Juma'a da ta gabata.

Amma bayan caccakar da ya sha, ya janye kalamansa inda ya zargi kafafen yada labarai da rashin fahimtar inda ya dosa.

Tattaunawarsa da BBC Hausa ta bayyana cewa babu rashin fahimta a cikin abinda jama'a ke yadawa, illa iyaka abinda ya sanar kenan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kwashe 'yan Maulidin kasa dake hanyar zuwa Sokoto

Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno
Batan biliyoyin kudin makamai: EFCC ta yi martani a kan ikirarin Monguno. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

A kan ko hukumar ta fara binciken lamarin, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren yace ba zai iya bada tabbacin cewa hukumar za ta binciki tsoffin hafsoshin tsaron ba.

Ya ce babu wata shaida da ta bayyana gaban hukumar wacce ke nuna cewa tsoffin hafsoshin tsaron sun kwashe kudin makamai kamar yadda mai bada shawara kan tsaron kasa yayi ikirari.

"Ba mu da wata shaida ko zargi. Muna aiki ne da abinda muka gani ba wai abinda za a ce zai iya yuwuwa ba," Uwujaren ya sanar da Daily Trust.

KU KARANTA: Rade-radin Rahama Sadau na neman miji: Jarumar tayi karin haske

A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Thunder Strike sun halaka 'yan bindiga biyu a wani smamen da suka kai cikin dare wurin babban titin Gwagwada zuwa Chikun dake karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, wannan na kunshe ne a wata takarda da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ya fitar a ranar Asabar.

Yace kamar yadda dakarun suka sanar, rundunar ta yi amfani da damar da ta samu wurin bibiyar kaiwa da kawowar 'yan bindigan.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng