Hukumar Kiyaye Haɗurra Ta Ƙasa Ta Kama Masu Laifi 10,455 A Cikin Watanni Biyu
- Hukumar kare haɗurra ta ƙasa ta bayyana cewa ta kama masu laifi 10,455 a jihar Lagos cikin watanni biyu kacal
- Shugaban hukumar reshen jihar Lagos, Mr Olusegun Ogungbemide, ya bayyana haka a wata fira da ya yi da NAN
- Ya kuma ƙara da cewa hukumar zata cigaba da gudanar da aikinta a jihar yadda yakamata musamman a manyan hanyoyi
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa ta bayyana cewa ta cafke masu laifi akan hanya 10,455 a jihar Lagos tsakanin watan Janairu da Fabrairu na wannan shekarar.
Shugaban hukumar reshen jihar Lagos, Mr Olusegun Ogungbemide ya faɗi haka yayin da yake zantawa da NAN ranar Lahadi a Lagos, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)
A bayaninsa, shugaban yace: "A watan Janairun wannan shekarar mun kama masu laifin da suka kai 4,686 da aikata laifuka 5,258."
"Amma a watan Fabrairu mun kama masu laifi 4,399 da aikata laifuffuka 5,197," inji shugaban hukumar.
KARANTA ANAN: Da duminsa: Jami'an tsaro sun sake dakile harin 'yan bindiga na yunkurin sace dalibai 307 a Kaduna
Ya kuma ƙara da cewa, hukumar na gudanar da aikinta ne a Lagos, kuma ana kokarin kiyaye duk wasu abubuwa da be kamata ba.
"Muna kokarin bin umarnin aikin mu yadda yakamata wajen cire abubuwan hawa marasa inganci domin rage aukuwar haɗurra a manyan hanyoyi," a cewarsa.
Daga ƙarshe ya roki masu abun hawa da suyi kokarin mallakar takardar shedar tuƙa abun hawa, yana mai bayyana cewa jami'an su zasu cigaba da kama waɗanda basu da wannan takardar.
A wani labarin kuma wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Shida Duk 'Yan Gida Ɗaya a Jihar Osun
'Yan bindigan sun farma garin Wasinmi, dake kan hanyar Ife/Ibadan da tsakiyar dare inda suka fara harbi kan me uwa da wabi
Hukumar 'yan sandan jihar ta bakin me magana da yawunta ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta tabbatar da kisan mutum shida 'yan gida ɗaya.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, Ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Yayi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha ɗake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77
Asali: Legit.ng