Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun afka makarantar firamare a Kaduna, sun kwashe dalibai da Malamai

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun afka makarantar firamare a Kaduna, sun kwashe dalibai da Malamai

Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai da malamai a makarantar firamaren gwamnati dake Rama, karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta samu labari daga bakin yan garin Rama inda suka bayyana cewa an kwashe yaran ne lokacin da suke zuwa makaranta misalin karfe 9 na safiyar Litinin, 15 ga Maris, 2021.

Kwamishanan tsaro dda harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya tabbatar da wannan labarin hakan a jawabin da ya saki.

Wani mazaunin garin, Abdulsalam Adam, ya ce yan bindiga sun dira garin kan babura kimanin 12.

"Na samu labarin an sace malamai uku da wasu dalibai amma muna kokarin tabbatar da gaskiyar lamarin. Yanzu haka yan banganmu sun bazama neman yan bindigan," yace.

"Muna makarantan yanzu haka, abinda muke kokarin yi shine lalube cikin dajin saboda wasu yaran sun gudu. Saboda haka bamu san adadin da aka sace ba yanzu."

Wani mazaunin, Mai Saje Rama, ya bayyanawa Daily Trust cewa: "Akwai wani mahaifi mai suna Halilu. Ya ce ya gansu sun dauke yaronsa kan babur. Muna makarantan yanzu kuma mun sanar da jami'an tsaro amma basu iso ba har yanzu."

Mohammadu Birnin Gwari, wani dan garin yace an sace kannensa biyu Umar Hassan da Rabiu Salisu Takau.

A bangaren gwamnatin jihar, Samuel Aruwan ya ce suna kan binciken adadin dalibai da malaman da aka sace kuma ta saki jawabi na musamman kai.

Yanzu-yanzu: Yan bindiga afka makarantar firamare a Kaduna, sun kwashe dalibai da Malamai
Yanzu-yanzu: Yan bindiga afka makarantar firamare a Kaduna, sun kwashe dalibai da Malamai
Asali: Original

Asali: Legit.ng

Online view pixel