Gobara ta yi kaca-kaca da ofisoshin soji 11 a jihar Kano

Gobara ta yi kaca-kaca da ofisoshin soji 11 a jihar Kano

- Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta shaida cewa, ta kashe wata wuta da ta kona ofisoshin soji

- A cewar sanarwar, hukumar ta kashe wutar a wani gini, in da ta cinye ofisoshi 11 nan take

- Hukumar ta bayyana cewa, ta yi nasarar kashe wutar, tare da binciken musabbabin kamarwarta

Hukumar kashe gobara ta Jihar Kano ta ce ta kashe wata gobara da ta kone ofisoshi guda 11 kurmus a sansanin sojoji na Bukavo da ke jihar.

Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ranar Juma'a, a cewar rahoton kamfanin labarai na NAN.

KU KARANTA: Da duminsa: Dimeji Bankole ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Gobara ta yi kaca-kaca da ofisoshin soji 11 a jihar Kano
Gobara ta yi kaca-kaca da ofisoshin soji 11 a jihar Kano Hoto: Naija News
Asali: UGC

Yusuf ya ce wutar wadda ta tashi da misalin ƙarfe 9:10 na dare, ta lalata wurin ajiyar kayayyaki guda hudu da kuma bandaki a ginin.

"Muna samun labari, nan take muka tura tawagarmu zuwa wurin da ƙarfe 9:19," in ji shi.

Ya kara da cewa an kashe wutar kuma ba a samu asarar rayuka ba. Ana kan bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, a cewarsa.

KU KARANTA: Tuna baya: Buhari yace an yi na karshe daga kan daliban Jangebe, sai kuma ga na Kaduna

A wani labarin, Sojojin rundunar gaggawa ta 1 na rundunar Sojin Najeriya sun dakile wani yunkuri da wasu 'yan bindiga suka yi don sace daliban makarantar Sakandaren Kasa da Kasa ta Turkiyya da ke Rigachikun, Jihar Kaduna, in ji Sojojin, The Nation ta ruwaito.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar Birgediya Janar Mohammed Yerima, a cikin wata sanarwa, ya yi bayanin: “Yin aiki da wata shawara kan abin da ke gabatowa na sace daliban makarantar, sojoji da sauri suka hada kai don kare makarantar daga‘ yan bindiga.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel