Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga a wani yankin Neja

Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga a wani yankin Neja

- Sakataren karamar hukumar Shiroro ya bayyana cewa, sun kashe kudaden domin yakar 'yan bindiga

- A cewarsa, karamar hukumar ta kashe N14m kan bokaye da 'yan banga domin fatattakar 'yan bindiga

- Sai dai, da alamu sakataren ya nuna nadama kan kashe kudaden bayan amsa wasu tambayoyi

Sakataren karamar hukumar Shiroro a jihar Neja, Adams Kefas, ya bayyana cewa an biya Naira miliyan 14 ga masu ruhanai da 'yan banga don yaki da 'yan bindiga a karamar hukumar, The Nation ta ruwaito.

Kefas ya ce an kawo wasu daga cikin masu ruhanan ne daga Akare a karamar hukumar Wushishi a jihar Neja wasu kuma daga karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Ya yi magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga Mai Shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik ta Kwamitin Shari’a da ke binciken dakatar da shugaban karamar hukumar Shiroro, Suleiman Dauda Chukuba, kan koke a kan zargin karkatar da kudi N50m.

KU KARANTA: Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kara zama abin tsoro a Kaduna

Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga, wani yankin Neja
Mun biya bokaye da 'yan banga N14m don yaki da 'yan bindiga, a wani yankin Neja Hoto: Research Gate
Asali: UGC

Ya ce an kawo wasu gungun ’yan banga daga karamar hukumar Shiroro yayin da aka kawo wasu daga karamar hukumar Chikun don taimakawa wajen magance matsalar rashin tsaro a karamar hukumar.

Karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja ta kasance cibiyar matattarar rashin tsaro da hare-haren 'yan bindiga a cikin jihar, da ake samun rahoton hare-haren da ake kaiwa a kan al'ummomi.

Kefas ya ce, an yi amfani da hadin gwiwar masu ruhanan ne bisa umarnin shugaban karamar hukumar, yana mai cewa shawarar ta biyo bayan shawarar da mazauna yankin suka bayar ne.

Ya ce masu ba da shawarar sun fada musu cewa yawancin al'ummomin da 'yan bindigan ke kaiwa hari sun hada kai da masu ruhanai kuma sun yi nasarar magance matsalolin tsaro a cikin al'ummomin.

Ya ce da farko ba a gaya masa cewa zai tattauna da masu ruhanai ba har sai da ya isa wurin.

A cewarsa: “Har sai da na isa wurin na san zan yi hulda da masu ruhanai.

"Daga nan ban iya komai ba face yin abin da na yi na taimakawa yankina don shawo kan kalubalen tsaro da mutanenmu ke fuskanta a kullum."

Shugaban Hukumar, Mai shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik, ta yi wa shugaban raddi game da rashin kula da kudaden da yake kashewa bayan ta yi wa shugaban tambayoyi, wanda ya yarda cewa an kashe kudi a kan ’yan banga da masu ruhanai.

KU KARANTA: Shugaban kasar Argentina ya sha ruwan duwatsu daga 'yan zanga-zanga a kasarsa

A wani labarin, Akalla dalibai 307 aka ceto yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati dake Ikara a karamar hukumar Ikara da ke Kaduna a safiyar ranar Lahadi, The Nation ta ruwaito.

Kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar harin.

A cewarsa, "Dalibai 307 ne aka samu nasarar kubutar da su ba tare da wani rauni ba" daga sojojin da suka dakile yunkurin satar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.