Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi

Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi

- Hukumar NYSC ta bayyana cewa, ya zama dole ga matasa 'yan bautan kasa su rigakafin Korona

- Shugaban hukumar ta NYSC ya shaidawa wata jarida wannan batu a yau, ranar Alhamis

- Shugaban ya tabbatar da cewa za a fara gudanar da allurar rigakafin a kan 'yan rukunin Batch A

Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidiman ta kammala shirye-shirye don ba da allurar rigakafin Korona ta AstraZeneca, ga dubunnan mambobin bautan kasar na Batch A 2021 wadanda yanzu haka ke kan aikinsu a dukkan sansanoni 37 a fadin kasar.

An samu labarin cewa hukumomin NYSC sun hadu da kwamitin shugaban kasa kan Korona a Abuja don amincewa sannan za su kuma hadu da Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko, wani sashe na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya kan shirin.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi
Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Da yake magana da SaharaReporters, Darakta-Janar na NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, ya tabbatar da shirin bayar da rigakafin Korona ga mambobin NYSC.

Tuni, NYSC yayin da take ba da shirin gabatarwa ga Batch A, mambobin kungiyar Stream One suka nemi su yi rajistar gwajin Korona a kan kafar ta ta kuma kawo takardar shaidar yin gwajin zuwa sansanin don gudanar ayyukansu.

A ranar Alhamis a wani sako da ya aika wa SaharaReporters kan allurar rigakafin ‘yan bautar kasa a sansanoni, DG din ya amsa da cewa,

“Tabbas. Akwai alƙawari tsakani na da Babban Daraktan Hukumar Kula da Kiwon Lafiya a Matakin Farko. Na kuma ambata hakan ga Shugaban PTF din ma. ”

KU KARANTA: Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki

A wani lababrin, Karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta tilasta wa kowace jiha ta karbi alluran Korona ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar dawata hira da jaridar Punch. Mamora yana mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi cewa ba zata sabu ba ya yi alluran rigakafin, ya kara da cewa mazauna jiharsa ba "aladu bane"

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel