Hukumar NAFDAC ta kusa kammala gwajin magungunan gargajiya don magance Korona

Hukumar NAFDAC ta kusa kammala gwajin magungunan gargajiya don magance Korona

- Biyo bayan fara riga-kafin Korona, NAFDAC ta shaida cewa tana kan bincike kan wasu magungunan gargajiya

- Ana sa ran magungunan gargajiyar zasu iya magance kwayar cutar Korona idan aka yi amfani dasu

- A cewar hukumar, gwamnati ta samar da shiri na bincike da ake da yakinin samun nasara kan maganin na Korona

Hukumar NAFDAC mai sa ido kan ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta ce ana nan ana ta gwajin magungunan gargajiya 14 a kasar don samar magani kan kwayar cutar Korona, BBC Hausa ta ruwaito.

Shugabar hukumar Farfesa Adeyeye ta ce magungunan tuni sun wuce matakin farko na gwaji, kawo yanzu kuma ana duba yiwuwar amfani da su kan magance kwayar cutar ta Korona.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona

Hukumar NAFDAC ta fara binciken maganin gargajiya don magance Korona
Masana maganin gargajiya | Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Ta ce "a yanzu mun amince da wadannan magunguna 14, mun tabbatar ba sa yi wa jikin dan Adam illa amma ba mu san yadda za su yi aiki kan kwayar cutar Korona ba shi ya sa za mu ci gaba da bincike a kan su," a cewarta.

Ta kuma ce gwamnati ta samar da wani shiri na bincike inda ta ce tana da yakinin za a samu nasara daga cikin magungunan wadanda za su iya kashe kwayar cutar Korona gaba daya.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta amince da rigakafin Korona, allurar har ta iso jihar

A wani lababrin, Shugaban jami’ar Adeleke, Farfesa Solomon Adebiola, ya bayyana cewa riga-kafin kwayar cutar COVID-19 da masana kimiyya na Najeriya suka kirkiro a halin yanzu tana matakin gwaji na asibiti, Vanguard News ta ruwaito.

Ya kara da cewa allurar, wacce Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince da ita kuma ta sami goyon bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta samu ne daga wani masanin kimiyya daga Jami’ar Adeleke, Dokta Oladipo Kolawole, tare da hadin gwiwar wasu daga wasu jami’o’i biyar na kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel