Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC tayi wani babban Kamu a jihar Ogun

Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC tayi wani babban Kamu a jihar Ogun

- Wani babban jigo a jam'iyyar PDP ya canza sheƙa izuwa jam'iyyar APC a jihar Ogun

- Tsohon ɗan takarar sanata a zaɓen da ya gabata ƙarƙashin jam'iyyar PDP ya fice daga jami'iyyar zuwa APC

- Ya bayyana cewa, shi dama can ɗan jam'iyyar APC ne, kuma ya dawo gida ne domin ya bawa gwamnan Ogun gudummuwarsa a kan ƙudirinsa na kawo cigaba a jihar

Ɗan takarar sanata daga mazaɓar Ogun ta gabas ƙarƙashin inuwar jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata, Adeola Sosanwo, ya canza sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin ƙasar nan.

Sosanwo, ya bayyana cewa ya yanke wannan shawarar ne domin yazo su haɗa gwuiwa da gwamnan jihar Ogun wajen kawo cigaba a faɗin jihar.

KARANTA ANAN: An yi an gama: Dalilin Gwamnatin Buhari na dakatar da ba Matasa tallafin kudi - Ministan wasanni

A jawabinsa, Addola Sosanwo ya ce:

"Daman can ni ɗan jam'iyyar APC ne, amma PDP ta yaudareni duk da cewa ni ba wani sananne bane a ƙarƙashin gwamnatin data shuɗe ta tsohon gwamna, Senator Ibikunle Amosun."

Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC tayi wani babban Kamu a jihar Ogun
Zaɓen 2023: Jam'iyyar APC tayi wani babban Kamu a jihar Ogun Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yan ta'addan ISWAP sun kaiwa Soji harin kwantan bauna, sun kashe jami'ai 19

"Saidai duk da haka na yanke shawarar dawowa APC ne don nuna goyon bayana ga ɗan uwan mu gwamnan jihar Ogun, Prince Dapo Abiodun a kan kudirin sa na gyara jihar daga halin da ya same ta," a cewar tsohon ɗan takarar.

Ya kuma ƙara da jinjinawa gwaman kan dawo da tsarin kyakkyawan shugabancin jihar domin inganta tattalin arziƙin jihar. Punch ta ruwito.

Sosanwo ya ƙara da bada misali inda yake cewa:

"Kalli ƙudirin gwaman na sake farfaɗo da filin jirgin sama na Agro-Cargo dake a Iperu Remo, da kuma sake gina hanyoyi masu yawa a faɗin jihar, kamar hanyar Epe - Ijebu, wadda ankusa kammala ta."

A wani labarin kuma Shugabannin hafsun soji sun sake dira jihar Borno don fatattakar Boko Haram

Shugabannin hafsoshin tsaron Najeriya sun sake dira jihar Borno a karo na biyu don magance matsalar tsaro.

Manufar ziyarar tasu ta biyu yana da nasaba da tantance halin da ake ciki na rashin tsaro a jihar

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel