Yan ta'addan ISWAP sun kaiwa Soji harin kwantan bauna, sun kashe jami'ai 19
Yan ta'adda ISWAP sun kai wa tawagar motocin rundunar Soji harin kwantan bauna a jihar Borno inda suka hallaka Soji 15 tare da yan banga hudu, majiyoyi sun bayyana ranar Asabar.
Yan ta'addan sun kai wannan hari ne kusa da Gudumbali a yankin tafkin Chadi ranar Alhamis, cewar majiyoyin.
Wani jami'in Soja wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa AFP cewa "mun rasa Sojoji 15 da CJTF hudu a harin da yan ta'adda suka kai a dajin dake kusa da Gudumbali."
Ya kara da cewa akalla dakaru 13 sun jigara a harin.
Tawagar motocin Soji 10 na kan hanyar zuwa Gudumbali ne daga garin Kukawa don kaiwa yan ta'addan farmaki sai aka bude musu wuta, cewar wata majiya daban.
A ranar Asabar, kungiyar masu tada kayar bayan ISWAP sun dau alhakin wannan hari.
An kafa ISWAP ne bayan ballewar Boko Haram a 2016.
Yan ta'addan kungiyar sun shahara da kaiwa Sojoji hari mazauninsu tare da garkuwa da matafiya a kan hanya suna kashesu.
Asali: Legit.ng