Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji

Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji

- Sauran daliban kwalejin harkar noma da aka sace cikin dare an kwashesu zuwa barikin sojoji

- Majiya daga rundunar sojin tace kokarin dakarun sojin sama da na kasa ne yasa harin bai kazanta ba

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna yace sojoji da 'yan sanda suna kokarin bin sahun daliban don ceto su

Ragowar daliban kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Afaka a Mando, jihar Kaduna an kwashesu zuwa barikin Div 1 Garrison Command a Kaduna.

Legit.ng ta ruwaito yadda 'yan bindiga suka shiga makarantar inda suka kwashe dalibai mata.

Wata majiya daga rundunar soji ta sanar da Daily Trust cewa ba don kokarin jami'an rundunar sojin sama ba da na Div 1 dake Kaduna, da harin sai ya fi haka kazanta.

KU KARANTA: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji
Da duminsa: Ragowar daliban makarantar da 'yan bindiga suka kai farmaki sun koma barikin sojoji
Asali: Original

Majiyar wacce ta bukaci a boye sunanta, ta ce an ceci wasu daliban yayin hari amma masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da wasu wadanda ba a tabbatar da yawansu ba.

ASP Mohammed Jalige, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ya tabbatar da aukuwar lamarin amma yace har yanzu ba a san yawan daliban da aka sace ba.

"Bamu da bayanin yawan daliban da aka sace," ya sanar da manema labarai inda ya kara da cewa 'yan sanda da sojoji na kokarin bin sahun wadanda aka sace domin ceto su.

KU KARANTA: Kasaitattun fadar sarakuna 6 a Najeriya da kyawawan hotunansu

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya jaddada cewa shi ya baiwa shugabannin tsaron kasar nan umarnin su matsantawa 'yan ta'adda, tare da harbe duk wanda suka kama dauke da AK-47 ba bisa ka'ida ba.

Shugaban kasan ya sanar da hakan a taron da yayi da majalisar sarakunan gargajiya a fadarsa dake Abuja wanda manyan sarakunan kasar nan suka samu halarta.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, taron ya samu halartar mai bada shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, darakta janar na hukumar jami'an tsaron farin kaya, Yusuf Bichi da darakta janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel