Ganawar Gumi da 'yan bindiga: Sun sha alwashin addabar El-Rufai da jihar Kaduna

Ganawar Gumi da 'yan bindiga: Sun sha alwashin addabar El-Rufai da jihar Kaduna

- A yau Juma'a ne jihar Kaduna suka tashi da mummunan labarin sace dalibai mata

- An gano cewa 'yan bindiga sun sha alwashin addabar El-Rufai da Kaduna a ganawarsu da Gumi

- Gwamnan Kaduna ya sha alwashin ganin bayan 'yan bindiga kuma ba zai taba yin sasanci dasu ba

A ranar Juma'a ne jihar Kaduna ta tashi da mummunan labarin sace dalibai mata a kwalejin harkar noma da gandun dabbobi da ke Mando a jihar Kaduna.

Makarantar na da nisan kasa da kilomita 15 daga makarantar horar da hafsoshin soji dake Kaduna (NDA).

A ranar Alhamis ne 'yan bindiga suka kai hari kananan hukumomin Igabi, Giwa da Chikun inda suka halaka mutane bakwai.

An gano cewa 'yan bindiga sun raunata wasu tare da sace shanu 20.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai

Ganawar Gumi da 'yan bindiga: Sun sha alwashin addabar El-Rufai da jihar Kaduna
Ganawar Gumi da 'yan bindiga: Sun sha alwashin addabar El-Rufai da jihar Kaduna. Hoto daga @SaharaReporters
Asali: Twitter

Wannan na faruwa ne bayan mako uku da 'yan bindigan dake Tegina a jihar Neja da Birnin Gwari dake jihar Kaduna suka gana da fitaccen malami, Sheikh Ahmad Gumi kuma suka sha alwashin addabar Gwamna Nasir El-Rufai.

A watan Fabrairu ne El-Rufai yace duk wani dan bindiga da aka kama a jihar ba za a sassauta masa ba domin babu batun sasanci tsakaninsa dasu.

Ya ki amincewa da shawarar Gumi inda yace a yi wa 'yan bindiga afuwa kuma a saka musu da sha tara ta arziki.

Gwamnan yace 'yan bindigan ba za su so barin garkuwa da mutane ba ganin cewa hakan na kawo musu kudi.

"Duk wanda yayi tunanin cewa bafulatanin da ya saba garkuwa da mutane yana karbar miliyoyin naira, zai koma tsohuwar rayuwarsa yana samun N100,000 bayan ya siyar da sa daya a shekara, ya yaudari kansa," El-Rufai yace.

KU KARANTA: Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya jaddada cewa shi ya baiwa shugabannin tsaron kasar nan umarnin su matsantawa 'yan ta'adda, tare da harbe duk wanda suka kama dauke da AK-47 ba bisa ka'ida ba.

Shugaban kasan ya sanar da hakan a taron da yayi da majalisar sarakunan gargajiya a fadarsa dake Abuja wanda manyan sarakunan kasar nan suka samu halarta.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, taron ya samu halartar mai bada shawara kan tsaron kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, Sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, darakta janar na hukumar jami'an tsaron farin kaya, Yusuf Bichi da darakta janar na NIA, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel