Bayan yin allurar Korona, gwamnan Bauchi ya roki Buhari ya nemo kudin siyan kari
- Gwamna jihar Bauchi a yau ya karbi kaso na farko na allurar rigakafin kwayar cutar Korona
- Gwamnan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta samo kudaden sayen cikon allurar
- Hakazalika ya bayyana dalilan da yasa aka fara yi wa shugabanni allurar rigakafin ta Korona
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a ranar Asabar, bayan yin allurar Korona taAztraZeneca da aka kawo wa jihar a baya, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta samo kudade domin samun isassun alluran rigakafi ga yawan mutanen kasar, Vanguard News ta ruwaito.
A cewar gwamnan wanda matar sa da wasu mukarraban gwamnatin jihar suka hada hannu a gidan gwamnatin Bauchi, jihar ta Bauchi mai kimanin mutane miliyan 8 an ba ta alluran rigakafi 80,570 ne kawai daga Hukumar raya Lafiya ta Kasa a matakin farko.
KU KARANTA: Kwana uku a jere 'yan bindiga na kai hari kauyen 'Yar Nasarawar-Akubu a Zamfara
“Ina son yin roko a madadin 'yan Najeriya cewa wannan allurar rigakafin bata isa ba. Ba za mu iya yin wasan siyasa da lafiyarmu ba. Najeriya tana da wadatar da za ta sayi allurar rigakafi, bai kamata mu zama kasa mabaraciya ba.
"Ina kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbata cewa mun nemi kayan aiki, ba dogaro da Covax cewa za ta iya biya bukatun dukkan yawan mu ba."
Gwamnan ya nuna godiyarsa ga Allah da ya rayashi ya kubuta daga illar wannan annoba ta kwayar cutar Korona. Hakazalika ya jaddada manufar fara yi wa shugabanni allurar ta Korona.
"Amma har yanzu bai kai ga Uhuru ba, mun zo nan ne kawai a matsayin shugabannin da za a yi musu wannan rigakafin don nuna cewa babu wata illa a ciki ta yadda za mu samu damar jan hankalin al'umma.
"Tabbas, babban burinmu shi ne jami'an kiwon lafiya wadanda ke sahun gaba wadanda suka fi kusa da matsaloli da kalubalen wannan bala'in. Bayan su, akwai sauran ma'aikatan kiwon lafiya, kuma mu shugabannin ne wadanda za su nuna misali,” inji shi.
KU KARANTA: Gobara ta yi kaca-kaca da ofisoshin soji 11 a jihar Kano
A wani labarin, Hukumar NAFDAC mai sa ido kan ingancin abinci da magunguna a Najeriya ta ce ana nan ana ta gwajin magungunan gargajiya 14 a kasar don samar magani kan kwayar cutar Korona, BBC Hausa ta ruwaito.
Shugabar hukumar Farfesa Adeyeye ta ce magungunan tuni sun wuce matakin farko na gwaji, kawo yanzu kuma ana duba yiwuwar amfani da su kan magance kwayar cutar ta Korona.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng