Kotun daukaka kara ta wanke matar da ake zargi da sheke mijinta ta hanyar yi wa mijinta allurar guba
- Kotun daukaka kara ta yankin Makurdi ta dakatar da hukuncin yanke wa matar dagacin wani kauye hukuncin kisa
- Babbar kotun jihar Nasarawa ta yanke wa Amina hukuncin ne bayan zargin da ake mata na yi wa mijinta allurar guba
- Ana zargin bayan tayi masa allurar ne a 2018 Adamu Zubairu, wanda shine dagacin kauyen Gom Mama dake karamar hukumar Wamba ya rasa ransa
Kotun daukaka kara dake yankin Makurdi ta dakatar da jaddada yankewa Amina Zubairu, matar dagacin wani kauye hukuncin kisan da karamar kotu ta yanke mata.
Wannan ya biyo bayan daukaka kara da tayi shekaru biyu bayan babbar kotun dake zama a Lafia, jihar Nasarawa ta yanke mata hukuncin kisa.
Karamar kotun ta yanke wa Amina hukuncin kisa tun 2018 bisa zargin kashe Adamu Zubairu, wanda a lokacin shine dagacin kauyen Gom Mama dake karamar hukumar Wamba dake jihar Nasarawa.
KU KARANTA: Ya zama dole mu matsantawa 'yan ta'adda, Buhari ga sarakunan gargajiya
Kamar yadda Channels TV ta wallafa, ana zarginta da yi wa mijinta allurar guba a 2014 wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Sakamakon kin amincewarta da hukuncin kotun, ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara don ta sauya hukuncin da karamar kotun ta yanke mata.
Kotun daukaka kara a zamanta na ranar 12 ga watan Maris na 2021, ta ce karamar kotun ta yanke hukuncin ne bisa rashin tabbatar da shaidu inda ta yanke mata hukuncin kisa a 11 ga watan Disamban 2018.
Lauyan mai daukaka kara, Shikammah Sheltu, ya yi na'am da hukuncin kotun daukaka kara.
Ya kuma mika godiyarsa ga kotun ta yadda tayi gaggawar duba shari'ar cikin kankanin lokaci.
A bangarensa, kwamishinan shari'a na jihar Nasarawa, Abdulkarim Kana, ya ce gwamnati za ta duba idan zai yuwu a daukaka karar ko kuma a fasa.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai
A wani labari na daban, majalisar wakilan tarayyar kasar nan tace ta talauce kuma kasafin da aka fitar mata ba dole ya amfani 'yan Najeriya ba.
Benjamin Kalu, mai magana da yawun majalisar ya sanar da manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, cewa 'yan majalisar na cikin tsananin "fatara yayin da suke kokarin sauke nauyin mazabunsu dake kansu."
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, 'yan majalisar tarayyar sun saba kokawa a kan albashin da ake biyansu na N800,000 da kuma N8.5 miliyan duk wata.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng