Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai

Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai

- 'Yan bindiga sun kai farmaki kwalejin harkar noma dake Mando a cikin garin Kaduna

- Sun kwashe dalibai mata masu tarin yawa amma basu dauka namiji ko daya ba

- Lamarin ya faru a daren Alhamis wurin karfe 11:30 zuwa 12 na dare inda aka dinga jin harbi

Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kwashe daliban kwalejin harkar noma da gandun daji dake Mando a cikin birnin Kaduna.

A halin yanzu ba a san yawan daliban da suka sace ba, sai dai kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan yace yana cikin makarantar kuma suna kan bincike.

Daya daga cikin daliban makarantar ta sanar da BBC cewa cikin dare 'yan bindigan suka kutsa makarantar.

A cewar dalibai, an kwashe rabin dalibai mata na makarantar kuma basu dauka ko namiji daya ba.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai
Da duminsa: 'Yan bindiga sun shiga wata makaranta a Kaduna, sun kwashe dalibai
Asali: Original

Wani mazunin unguwar Mando a jihar ta Kaduna ya bayyana cewa kusan karfe 11 da rabi na dare zuwa 12 sun rika jin harbi amma sun yi zaton a Makaratar Horar da Sojoji ta NDA ne ake yi.

Wani mutum mazaunin Mando a Kaduna yace wurin karfe 11:300 zuwa 12 suka dinga jin harbi amma a tsammaninsu makarantar horar da hafsoshin soji ne ake horar da dalibai.

"A wasu lokutan NDA su kan yi harbe-harbe cikin dare tunda dama dalibansu suke horarwa. Hakan kowa yayi tunani. Da safe da muka fita sallar subhi ne muka samu mugun labari," yace.

KU KARANTA: Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche

A wani labari na daban, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce 'yan bindiga sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya don haka ya zama dole a shafesu.

Ya ce ya zama dole gwamnati a kowanne mataki ta gaggauta ba tare da kasa a guiwa ba wurin kawo karshe al'amuran 'yan bindiga.

El-Rufai yayi wannan tsokacin ne a ranar Laraba yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 na jihar Kaduna, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng