Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo

Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo

- Tsohon kyakyawan basarake, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi zai angwance da sabuwar amarya

- A wani taro, an ga babban basaraken tare da amaryar mai suna Chioma wacce 'yar asalin gabas din kasar nan ce

- Basaraken yana da tarin mata wadanda suka kasance kyawawa masu cike da izzar sarauta

Dattijon basarake, Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ya samu zukekiyar amarya mai suna Chioma.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a daya daga cikin fitar da suka yi tare, Chioma, sabuwar amaryar an ganta a wani taro tare da dattijon basaraken.

Wannan ne karo na farko da babban basaraken zai angwance da zukekiyar budurwa daga yankin gabas na kasar nan duk da mata masu tarin yawa da ya mallaka.

KU KARANTA: Dole a shafe 'yan bindiga, sun kalubalanci karfin mulkin Najeriya, El-Rufai

Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo
Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo
Hotunan zukekiyar amaryar tsohon basarake, Alaafin na Oyo. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga da ke ikirarin sun tuba siyan makamai suke da kudaden da ake basu, Gwamnan Neja

A wani labari na daban, sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Bamalli da sarkin Birnin-Gwari, Alhaji Zubairu Maigwari II, sun ce mutanensu sun biya daruruwan miliyoyi a matsayin kudin fansa ga 'yan bindiga.

Sun sanar da hakan ne yayin gabatar da rahoton tsaro na 2020 ga Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, The Nation ta wallafa.

Maigwari ya ce: "Abun takaici ne da tashin hankali ka ga 'yan bindiga 200 zuwa 300 dauke da makamai sun zagaye kauye suna kashe jama'a tare da karbe kudadensu. Jama'armu sun biya daruruwan miliyoyin naira a matsayin kudin fansa."

Bamalli ya jinjinawa jami'an tsaro inda yace: "Muna da kalubale har yanzu a Zaria da Giwa saboda idan karfe 6 na yamma tayi ba a iya zuwa wasu yankuna. Wadannan wuraren suna da tsananin hatsari."

Sarkin Zangon-Kataf, Agwatyap, Dominic Yahaya, yace duk da yadda ake sace jama'a lokaci zuwa lokaci a yankinsa, kwamitin da ya kafa na neman zaman lafiya bai gaza ba.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel