Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power

Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power

- Biyo bayan rajistar neman aiki a karkashin shirin N-Power, za ci gaba da zaban wadanda suka cancanta

- Ministar Jin Kai da Harkokin Ci Gaban Jama'a ta bayyana haka ne a wani taron bude shirin

- Ta bayyana yadda tsarin zaben zai kasance da yadda aka tsara gwaji don wucewa mataki na gaba

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da fara tantance wadanda suka nemi aiki a karkashin N-Power a rukuni na uku, The Nation ta ruwaito.

Ministar Jin Kai da Harkokin Ci Gaban Jama'a Sadiya Farouq a bara ta sanar da cewa sama da mutum miliyan biyar aka karbi rajistarsu.

An bude kafar cika neman aikin a ranar Juma'a, 26 ga Yuni, 2020, an kuma rufe tsakar dare a ranar 8 ga Agusta, 2020.

A matsayin daya daga cikin matakan da za a bi na yadda za a zabi wadanda suka cancanta Ministar ta kaddamar da wata hanyar shiga wato National Social Investment Management System (NASIMS) don saukaka daidaitawa, turawa da gudanarwa.

KU KARANTA: Rigakafin Korona: Dole ne 'yan bautar kasa (NYSC) su yi allurar rigakafi

Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power
Gwamnatin tarayya ta fara zaban masu cin gajiyar shirin N-Power Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

Ta bayyana cewa duk masu neman aikin an kaurar dasu zuwa dandalin NASIMS, sannan ta kara da cewa za a bukaci su yi wata gajeriyar gwaji ta yanar gizo a matsayin bangare na tsarin zaben.

A cewar ta, shirin na rukuni na uku zai dauki tsawon watanni 12, tana mai karawa da cewa kowane mai cin gajiyar za a rika biyan sa albashi na N30,000 duk wata.

Ministar ta kuma danganta jinkirin da aka samu a dukkan ayyukan da barkewar Korona.

Ta nuna kwarin gwiwa cewa sabon dandalin zai magance matsaloli da damuwar da aka samu a baya.

Da take karin haske kan wasu abubuwa da ake tsammani daga masu bukatar, ta ce:

“Yayin da muke kaddamar da N-Power rukuni na uku a yau, ana bukatar duk masu neman N-Power rukuni na uku da su shiga kafar N-Power ta www.nasims.gov.ng tare da kuma sabunta bayanan su.
Biyo bayan haka zasu iya ci gaba zuwa matakin gaba na yin gwaji kafin su iya wucewa matakin zabe na gaba. Bayani kan yadda ake shiga kafar za a aika ta sakon sms da imel zuwa ga masu neman aikin na rukuni na uku.

“Yana da kyau a sani cewa tsarin tantancewar na shirin N-Power an tsara shi ne bisa cancanta da wakilcin adalci a dukkan sassan kasar.

"Saboda haka, matakai da sharuddan zabin za su tabbatar da daidaito a yanki tare da wakilcin jinsi. Bugu da kari kuma, Ma'aikatar ta yi la'akari da wasu na musamman da suka hada da nakasassu.

KU KARANTA: Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki

A wani labarin, Babban bankin Nigeria, CBN, ta sake bude shafinta na TCF don bada rance ga wadanda suka fada matsin tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19.

Bankin bada bashi ga manoma ta NIRSAL ne ta sanar da hakan a ranar Litinin cikin wani sako da ta wallafa a Twitter.

CBN ta bullo da tsarin ne domin tallafawa jama'a, masu kananan sana'o'i da matsakaitan kamfanoni su farfado daga illar da annobar korona ta yi musu. Bankin NIRSAL ne ke da hakkin rabar da bashin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel