Namijin da ba zai iya ba budurwa N300K na kasuwanci ba, bai cancanci a aure shi ba, Uche
- Fitaccen tauraron fina-finan Nollywood, Uche Maduagwu ya gigita kafar sada zumunta da matsayarsa a kan miji nagari
- Jarumin yace in har namiji ba zai iya baiwa mace a kalla N300,000 ba domin kasuwanci, bai cancani a aure shi ba
- Wannan tsokacin yasa masoya da mabiyansa suka yi ca inda suka dinga tsokaci daban-daban a kan lamarin
Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Uche Maduagwu, ya sake gigita kafar sada zumuntar zamani da irin shawarwarinsa na soyayya.
Tauraron fina-finan an san shi da janyo cece-kuce da irin tsokacinsa tare da matsayoyinsa ta yadda ake gane miji nagari.
Kamar yadda Maduagwu ya sanar a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, in har namiji ba zai iya baiwa mace a kalla N300,000 ba domin fara kasuwanci, bai cancanci a aure shi ba.
KU KARANTA: Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai
Jarumin ya bukaci mata su ajiye soyayya a gefe sannan su rungumi shawararsa.
A kalamansa, "Ya ku 'yammata, manta da soyayya. Duk namjin da ba zai iya baku a kalla N300,000 ba domin fara kasuwanci ba, bai cancani a aure shi ba."
Ga wasu daga cikin tsokacin jama'a:
Ewatofunmi27 cewa tayi: "Toh wannan ne ma'anar soyayya?"
Wellchecked_sa cewa yayi: "Kana magana kamar wanda zai ya baiwa wani N300,000"
KU KARANTA: Bayan tura dakaru 6000 Zamfara, Buhari ya baiwa 'yan bindiga wa'adin mika makamai
A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun yi martanin gaggawa a harin da mayakan ta'addanci suka kai a daren Talata har babban birnin Maiduguri, jihar Borno.
Harin ya zo ne bayan makonni kadan da aka kaiwa Maiduguri mummunan hari inda 'yan ta'addan suka ratsa jami'an tsaron da ke birnin suka wurga bam wanda ya halaka a kalla mutum 15.
HumAngle ta gano cewa mazauna garin a daren Talata sun shiga dimuwa bayan da suka ji karar harbin bindigogi da tashin abubuwa masu fashewa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng