Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora

Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora

- Karamin ministan lafiya a Najeriya ya mayarwa gwamnan Kogi martani kan batun rigakafin Korona

- Ministan ya bayyana cewa, ba za a tilastawa jihar ta Kogi sai ta amice da yin rigakafin na Korona ba

- Hakazalika dukkan jihohin da basa so, su ma ba za a tilasta musu ba, ana yin allurar ne ga jihar da take so

Karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta tilasta wa kowace jiha ta karbi alluran Korona ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar dawata hira da jaridar Punch.

Mamora yana mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi cewa ba zata sabu ba ya yi alluran rigakafin, ya kara da cewa mazauna jiharsa ba "aladu bane"

Najeriya ta fitar da shirinta na rigakafin kamuwa da kwayar cutar a ranar Juma'a tare da kimanin allurai miliyan hudu na AstraZeneca / Oxford ta Korona.

KU KARANTA: Yanzun nan: Gwamna Dapo Abiodun ya zama gwamna na farko da ya fara yin rigakafin Korona

Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora
Gwamnatin Tarayya ba zata tirsasa rigakafin Korona a Kogi ba, in ji Mamora Hoto: The Punch News
Asali: UGC

An yi wa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo rigakafin cutar a ranar Asabar don nuna lafiyar allurar. Gwamnonin jihohi suma sun fara yin alluran domin karfafa gwiwar ‘yan kasar su na aminta da alluran.

Da aka tambaye shi a ranar Talata ko Gwamnatin Tarayya za ta bai wa Jihar Kogi allurar rigakafin ganin abin da gwamnan ya ce, Ministan ya ce,

“Dole ne mu auna duk abin da ke ciki. Ba za mu tilasta wa kowa ya yi allurar ba. Muna kuma sane da gaskiyar cewa har zuwa yanzu, ba mu da isassun allurar rigakafin.

“Don haka, a takaice, idan wata jiha ta hanyar gwamna ko ta wani mutum da ke wani mukami ya ce ba a son allurar rigakafin a jihohinsu, ba za mu tilasta hakan ba.

“Babbar alkiblarmu zata tafi ga jihohin da suke so kuma suke a shirye kuma har ma suka gabatar da bukatar yin alluran.

"Ko da Littafi Mai Tsarki ya ce, 'Ka tambaya kuma za a baka'. Za mu ba wa jihohin da suka nemi hakan. Idan wata jiha ta yanke shawara ba za ta nemi hakan ba, ba za mu tilasta wa jihar ta nemi hakan ba.”

KU KARANTA: Bayan taron addu'a, Sarkin Kano yace 'yan Najeriya da su amince da rigakafin Korona

A wani labarin, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha ya ce ba wanda zai tsira daga kamuwa da cutar Korona har sai an yiwa kowa rigakafi, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Mutspaha ya fadi haka ne a ranar Juma'a yayin gabatar da alluran rigakafin COVID-19 a Asibitin Kasa da ke Abuja, babban birnin kasar. “A gare mu a Najeriya da kuma kasashen duniya gaba daya, darussan da za a dauka daga wannan rashin nuna wariyar ta kwayar suna da yawa.

Sun hada da gaskiyar cewa dole ne mu kusanci yin allurar rigakafin tare da hadin kai ga manufar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel