Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki

Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki

- Kasar Saudiyya ta yanke shawarar barin a dama da mata a fannoni daban daban na aiki a kasar

- Wata hukuma a kasar ta koka kan yadda ake ware mata a wasu guraben aiki da ake tallatawa

- Kasar ta bada umarnin daidaito wajen bude guraben aiki ga mata kamar yadda aka bai wa maza dama

Ma'aikatar Ci gaban al'umma ta daular Saudiyya na aiki kan wata manufa mai yaki da nuna wariya da za a fara amfani da ita a kasar nan ba da jimawa ba, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

A cewar jaridar, manufar, wadda za ta haramta nuna wariya, irinta ce ta farko a kasar. Ta kuma ce ana matakin karshe na shirya ta kuma za a amince da ita nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA: Ba za ta sabu ba, ba zamu yi hayar mayaka daga kasashen waje ba, Gwamnatin Buhari

Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki
Daular Saudiyya za ta bai wa mata 'yancin gogayya da maza a fannin aiki Hoto: About Her
Asali: UGC

Kwanan nan ne hukumomin kasar suka samar da wani tsari na kai karar masu nuna wariya a wuraren aiki.

Haka kuma, ma'aikatar na kokari wurin kawo karshen nuna wariyar jinsi a biyan albashi da daukar aiki.

Ma'aikatar ta jaddada cewa duka 'yan kasar na da 'yancin yin aiki ba tare da nuna wariyar jinsi ko wani abu na daban ba. Don haka wuraren aiki su rika daidaito a lokacin daukar aiki ko wajen tallar guraben aikin.

Gargadin ma'aikatar ya zo ne bayan da wani kamfani ya wallafa gurbin aiki ga maza zalla a kasar.

Ta ce wannan ya saba wa dokokin kwadago ta kasar, kuma ta ce ko wane dan kasa mace ko namiji na da ikon yin duk aikin da ya so ya yi.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: An sace malaman makaranta da dalibansu a jihar Edo

A wani labarin, Shugaba/wadda ta assasa kungiyar mata ta Aspire, Barista Zainab Marwa-Abubakar, ta ce akwai yiwuwar mace ta gaji Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Ta fadi haka ne a ranar Lahadi a taron masu ruwa da tsaki na mata a Abuja. Shirin na daga cikin ayyukan bikin ranar mata ta duniya ta bana.

“Yayin da 2023 ke gabatowa, na yi imanin cewa mata za su ɗauki haƙƙinsu, a matsayinsu na shugabanni, masu tsara manufofi da masu yanke shawara a cikin wannan rawar neman mulki.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel