Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa

Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa

- Wata shararriyar Barista a Njeriya ta shaidawa mata cewa, ta yiwu su tsayar da mace takarar shugabancin Najeriya

- A cewarta, mata na da jajircewar da ya dace wajen kawo wa kasa ci gaba, musamman a irin wannan yanayi

- Ta kuma shawarci mata da su koma yankunansu domin shiga siyasa dumu-dumu don a dama dasu

Shugaba/wadda ta assasa kungiyar mata ta Aspire, Barista Zainab Marwa-Abubakar, ta ce akwai yiwuwar mace ta gaji Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Ta fadi haka ne a ranar Lahadi a taron masu ruwa da tsaki na mata a Abuja. Shirin na daga cikin ayyukan bikin ranar mata ta duniya ta bana.

“Yayin da 2023 ke gabatowa, na yi imanin cewa mata za su ɗauki haƙƙinsu, a matsayinsu na shugabanni, masu tsara manufofi da masu yanke shawara a cikin wannan rawar neman mulki.

"A yanzu haka, ba mu gama haduwa ba har yanzu don zabar matar da za ta gaji Mai Girma, Shugaba Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Kasar Autria ta dakatar da yin rigakafin Korona na AstraZeneca saboda zargin mutuwa

Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa
Watakila mace ta gaji kujerar shugaba Buhari a zaben 2023, Zainab Marwa Hoto: Security King Nigeria
Asali: UGC

"Amma, me zai hana? Komai na iya faruwa, komai na iya yiwuwa, amma da lokaci mai zuwa,” in ji ta yayin da take amsa tambayar kan yiwuwar mace ta zama Shugaban Kasa a zaben 2023.

“Ku (mata) dole ne ku ilimantar da kanku, musamman saboda kasancewar duk siyasa ta gari ce.

"Don haka, dole ne ku je yankinku, ku haɗa kanku da ƙungiyar siyasa, siyasa ta, jam’iyyata, APC yanzu haka, tana rajistarta na jam'iyya da sake jaddadata a kewayen Najeriya. Don haka, lallai ne ku je ku yi rijista da jam'iyyar siyasa sannan ku fara tsarawa, koya da kuma aikatawa.”

A nata bangaren, Kodinetan kungiyar na kasa, Gift Johnbull, ta ce gina kasa wani aiki ne na hadin gwiwa kuma a zahiri matasa sune mahimman sinadari a gina ƙasa, saboda haka ake buƙatar matasa su shiga siyasa.

Ta ce ya kamata mata su yi imani da kansu kuma su san cewa su muhimman abubuwa ne wajen gina kasa.

KU KARANTA: Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna

A wani labarin, Wata kungiyar siyasa dake goyon bayan Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ta ce shi (Bello) zai magance matsalar rashin tsaro a Najeriya, tare da yin amfani da dabarun da ya yi amfani da su wajen kiyaye jihar sa lafiya, The Nation ta ruwaito.

Kungiyar ta bayyana gwamnan a matsayin wanda yafi kowa cancanta ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Kungiyar ta lura da fitowar Gwamnan zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar nan cewa zai yi amfani da dabarun da ya bi a Jihar Kogi don magance matsalolin tsaro na kasar.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel