Abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya bayan su sani bayan yin rigakafin Korona

Abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya bayan su sani bayan yin rigakafin Korona

- Hukumar NCDC ta shaidawa 'yan Najeriya matakan da zasu dauka biyo bayan yin rigakafin Korona

- Hukumar tace, yin allurar ba ya nufin jama'a zasu daina bin ka'idojin kiwon lafiya kwata-kwata

- Hakazalika, hukumar ta shawarci al'umma da su doge kan bin ka'idojin Korona bayan rigakafin

Najeriya, a makon da ya gabata ta samu isowar allurar rigakafin kwayar cutar Korona ta AstraZeneca a kokarin ta na yaki kwayar cutar.

Isowar allurar ke da wuya, gwamnatin kasar ta kaddamar da fara yin allurar ga ma'aikatan lafiya na sahun farko a kasar, kafin daga bisani shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo suka yi allurar a gaban kafafen yada labarai.

KU KARANTA: Majalisar wakilai ta nemi Buhari ya yi hayar mayakan waje don yakar Boko Haram

Abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya bayan sun yi rigakafin Korona
Abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya bayan sun yi rigakafin Korona Hoto: The Guardian
Source: UGC

A cikin makon nan, aka fara jigilar daukar allurar zuwa wasu johohi domin tabbatar da an yi allurar ga 'yan kasar.

Gwamnan jihar Ogun, shine gwamna na farko da ya fara karbar allurar a fadar jiharsa, yayin da a yau Laraba kuwa gwamnan jihar Kaduna da mataimakiyarsa su ma suka yi rigakafin.

Hukumar NCDC, ta wallafa abubuwan da ya kamata 'yan Najeriya su yi bayan yi musu allurar ta rigakafin Korona.

Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “Ba komai bane dan kun karbi allurar rigakafin, har yanzu kuna bukatar bin NPIs da sauran ka'idojin kiwon lafiyar jama'a. Wannan yana da matukar muhimmanci.” in ji Daraktan Kulawa da Ilimin Cututtuka.

1. Ku sanya takunkumin fuska

2. Ku wanke hannuwanka akoda yaushe

3. Ku kiyaye dokar nisantar jama'a

KU KARANTA: Labari mai dadi: Gwamnatin Buhari za ta rage kudin man fetur zuwa N100 a kowace lita

A wani labarin, A ci gaba da yin allurar rigakafin kwayar cutar Korona a Najeriya, a yau gwamnan jihar Kaduna ya karbi sashin farko na allurar rigakafin a jiharsa ta Kaduna.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta wallafa a shafin Twitter cewa, gwamnan ya yi allurar. An rubuta: "Malam Nasir @elrufai ya karbi kashi na farko na allurar rigakafin Korona na Astra Zeneca"

Hakazalika, mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna Dakta Hadiza Balarabe ita ma ta karbi kaso na farko na allurar rigakafin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit

Online view pixel