Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona

Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona

- Ana ci gaba da yin allurar rigakafin kwayar cutar Korona ta AstraZeneca a Najeriya

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya karbi kashin farko na allurar Korona

- Mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna, ita ma an yi mata allurar biyo bayan gwamnan

A ci gaba da yin allurar rigakafin kwayar cutar Korona a Najeriya, a yau gwamnan jihar Kaduna ya karbi sashin farko na allurar rigakafin a jiharsa ta Kaduna.

Gwamnatin jihar ta Kaduna ta wallafa a shafin Twitter cewa, gwamnan ya yi allurar.

An rubuta: "Malam Nasir @elrufai ya karbi kashi na farko na allurar rigakafin Korona na Astra Zeneca"

Hakazalika, mataimakiyar gwamnan jihar ta Kaduna Dakta Hadiza Balarabe ita ma ta karbi kaso na farko na allurar rigakafin.

KU KARANTA: Wata sabuwa: 'Yan bindiga sun sace mutane sama 55 a jihar Katsina

Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona
Da dumi-dumi: A yau an yi wa gwamna El-Rufai rigakafin Korona Hoto: @GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tuban muzuru 'yan bindiga ke yi su karbi kudinmu su siya makamai, gwamnan Neja

A wani labarin, Karamin Ministan Lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Gwamnatin Tarayya ba za ta tilasta wa kowace jiha ta karbi alluran Korona ba.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gabatar dawata hira da jaridar Punch. Mamora yana mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi cewa ba zata sabu ba ya yi alluran rigakafin, ya kara da cewa mazauna jiharsa ba "aladu bane"

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel