Labari da dumi-dumi: Fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba a 2021, ganga ta kai $71.3

Labari da dumi-dumi: Fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba a 2021, ganga ta kai $71.3

- Gangar danyen mai ya tashi a kasuwar Duniya a farkon makon nan

- Ana saida kowace gangar danyen mai a kan $71 a safiyar yau dinnan

- An shafe fiye da watanni 14 gangar mai ba ta yi irin wannan tashi ba

Jaridar CNBCTV ta rahoto cewa gangar danyen man fetur ya yi tashin da bai taba yi ba a kasuwannin Duniya a wannan shekarar ta 2021.

Rahotanni sun tabbatar da cewa a karon farko a 2021, gangar danyen fetur ya haura $70.

Abin da ake saida gangar danyen mai a kasuwar Duniya a yau shi ne $71.28. A kudinmu na gida, farashin gangar danyen zai kai kusan N30, 000.

Hakan na zuwa ne bayan kungiyar OPEC ta kasashen da ke da arzikin mai ta ki bada dama a kara adadin danyen man da za a rika hako wa a kullum.

KU KARANTA: Gwamnati ta nada kwamitin da zai tantance farashin man fetur

A makon da ya gabata, gangar danye man Brent ya kara daraja da 2%. Kudin kowace gangar danyen man fetur ya karu da $1.28 a ranar Laraba.

Wannan ya sa masanan tattalin arziki irinsu Norbert Rücker su ka fara haroro cewa farashin gangar mai zai doshi sama da $70 a tsakiyar shekarar bana.

Jaridar Economic times ta ce farashin man ya tashi sama da fiye da 2% a farkon makon nan ne sakamakon harin da aka kai wa kamfanin Aramco a Saudi.

Wannan shi ne mafi tsadan da farashin gangar danyen mai ya taba yi tun farkon shekarar 2019.

KU KARANTA: Farashin litar man fetur zai iya kai N185-N200 a gidajen mai

Labari da dumi-dumi: Fetur ya yi tsadar da bai taba yi ba a 2021, ganga ta kai $71.3
Danyen mai ya tashi Hoto: www.ft.com
Source: UGC

Rahotonni sun ce wannan canjin farashi da aka samu shi ne na farko a cikin sama da shekara guda da danyen man fetur ya zarce $70 a kasuwannin Duniya.

A cikin kowace gangar danyen mai, ana samun fiye da lita 158. Abin da tashin kudin yake nufi shi ne farashin litar mai da ba a tace ba ya haura N188 a kudin gida.

A makon da ya gabata kamfanin mai na kasa watau NNPC, ya ce babu karin farashin man fetur da za ayi a wannan watan na Maris kamar yadda ake tunani.

NNPC ya gargadi mutane a kan sayen mai da ake ta yi a tsorace har ana ta faman boye wa, ya ce ba za a gamu da wani karin farashin lita a watan Maris, 2021 ba.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng News

Online view pixel