Tuban muzuru 'yan bindiga ke yi su karbi kudinmu su siya makamai, gwamnan Neja

Tuban muzuru 'yan bindiga ke yi su karbi kudinmu su siya makamai, gwamnan Neja

- Gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa, 'yan bindiga yaudarar jihohi suke su karbe kudade

- Gwamnan yace, idan 'yan bindiga sun tuba sukan karbi kudi ne domin sayen karin bindigogi

- Gwamnan ya fahimci haka, ya kuma bayyana gwamnati ba za ta bai wa 'yan bindiga kudi ba

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani-Bello, ya ce 'yan bindiga sun yaudari jihar da ta yi imanin cewa sun tuba domin su samu kudin siyan karin makamai don ci gaba da hare-haren su, Leadership ta ruwaito.

Gwamnan ya ce dalili ke nan da yasa gwamnatin jihar ta toshe duk wata hanyar tattaunawa da masu aikata laifin, yana mai bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yaudari jihar da tuban muzuru don samun kudin da za su sayi karin makamai.

Sani-Bello ya ce bayan sun fahimci maganganun 'yan ta'addan, sun dakatar da duk wata hanyar tattaunawa da 'yan bindigar.

Amma duk da haka ya ce wadanda suka shirya tuba da gaske za a karbe su kuma a maida su cikin al'umma ba tare da an basu kudi ba.

Gwamnan wanda ya yi magana a ranar Alhamis yayin da yake tare da kungiyar ’yan banga a karamar hukumar Mariga ya ce,

KU KARANTA: Cin hanci da rashawa zan yaka ba mutane ba, shugaban EFCC Abdurrasheed Bawa

'Yan bindiga wayo suke mana su karbi kudin fansa domin sayen bindiga, gwamnan Neja
'Yan bindiga wayo suke mana su karbi kudin fansa domin sayen bindiga, gwamnan Neja Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

“Na zo nan ne don in yi wa ’yan banga godiya, in kara musu kwarin gwiwa sannan in kara bayar da goyon baya daga gwamnatin jihar don su ci gaba da tallafawa ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro a yakin da ake yi da ‘yan bindiga da sauran hanyoyin aikata laifi.”

“Duk wani dan bindiga da ya mika makamansa kuma ya tuba daga kazamar rayuwarsa za a gafarta masa, kuma a samar masa da hanyar rayuwa wanda ba lallai ne ya hada da duk wani tallafi na kudi ba.

"Duba da abinda ya faru, an gano cewa tubabbun 'yan bindigan, bayan sun tara kudi ta hanyar tattaunawar, za su sayi karin makamai su koma ga tsohuwar hanyar su ta 'yan ta'adda."

Yayin da yake yabawa kokarin 'yan banga a jihar, Gwamna Sani-Bello ya kara da cewa biyan diyya ga iyalan wadanda suka yi babbar sadaukarwar yana gudana kuma zai ci gaba da ci gaba.

Ya ce don inganta hare-haren da suke kai wa 'yan ta'adda, za a samar da Bindigogi masu sarrafa kansu da sauran manyan makamai ga 'yan banga.

Ya ba da tabbacin cewa babu wata barazana da za ta sa ya wargaza ’yan banga a jihar, yana mai cewa “ba za mu wargaza ’yan banga ba saboda; ko da 'yan bindiga sun kare, 'yan banga za su ci gaba da samar da tsaro a tsakanin al'umma."

KU KARANTA: Zamu bai wa Kiristocin Arewa mafakar siyasa a Biafra, Nnamdi Kanu

A wani labarin, Akalla, an sace mutane 55 a wasu hare-hare daban-daban da aka kai wa kauyukan Katsina.

‘Yan bindiga sun afka wa kauyen Katsalle da ke karamar Hukumar Sabuwa a daren Litinin, inda suka yi awon gaba da mutane 30, wadanda akasarinsu mata ne.

Wani mazaunin Katsalle ya shaida wa wakilin Daily Trust a waya cewa kusan 40 daga cikin ’yan bindigan sun isa kauyen da misalin karfe 12 na ranar Litinin, suna tafe akan babura.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.