Buhari ya baiwa 'yan bindiga watanni 2 su mika wuya, in ji Gwamnan Zamfara

Buhari ya baiwa 'yan bindiga watanni 2 su mika wuya, in ji Gwamnan Zamfara

- Shugaba Muhammadu Buhari ya tura rundunar sojoji mutum 6,000 jihar Zamfara don magance rashin tsaro

- Hakazalika, shugaban ya bai wa 'yan bindiga wa'adin watanni biyu da su gaggauta ajiye makamansu

- Gwamnan jihar Zamfara ya nuna jin dadinsa da matakin da shugaban kasan ya dauka don magance matsalar tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa ‘yan bindiga a Zamfara wa'adin watanni biyu su mika wuya, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya fada a cikin wani shiri da yammacin Talata, Daily Trust ta ruwaito.

Matawalle ya ce shugaban ya kuma bayar da umarnin tura dakaru 6,000 domin murkushe 'yan ta'addan idan suka kasa mika makamansu.

Gwamnan ya yi wannan bayanin ne 'yan sa'o'i kadan bayan da sarakunan gargajiya a jihar suka fada wa shugabannin hafsoshin tsaro, wadanda suka kawo ziyara jihar, cewa akwai 'yan fashi sama da 30,000 a dazukan Zamfara.

KU KARANTA: Sunday Igboho: Sai na kafa Jamhuriyar Oduduwa, kuma zan kashe Yarbawa masu hana ni kafin 2023

Buhari ya baiwa 'yan bindiga watanni 2 su mika wuya, in jiGwamnan Zamfara
Buhari ya baiwa 'yan bindiga watanni 2 su mika wuya, in jiGwamnan Zamfara Hoto: Vanguard News
Asali: UGC

Adadin da ya dara sojoji kasa da 10,000 da aka tura jihar don magance rashin tsaro na shekaru.

Umarnin da Shugaba Buhari ya bayar ya zo ne kimanin mako guda bayan ya ayyana Zamfara a matsayin yankin da jirgi ba zai tashi ba, dakatar da ayyukan hakar ma'adanai don dakatar da abin da jami'an fadar shugaban kasar suka bayyana da "ayyukan musayar makamai da zinariya".

A cikin shirinsa na watsa labarai a daren jiya, gwamnan na Zamfara ya ce ya kai ziyarar aiki ta kwanaki hudu a Abuja don yi wa Shugaba Buhari da sauran masu ruwa da tsaki bayanai masu muhimmanci game da halin tsaro a jiharsa.

“A tattaunawar da na yi da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma manyan hafsoshin tsaro a Abuja, an cimma matsaya cewa za a tura karin dakaru 6,000 don taimakawa kokarin da sauran jami’an tsaro ke yi na magance matsalolin tsaro a jihar.

“Nan ba da dadewa ba sojojin za su zo jihar domin gudanar da ayyukansu kuma muna godiya ga gwamnatin tarayya.

"Shugaban kasar ya amince da wani lokaci wanda a ciki ne ya kamata 'yan ta'addan da ke tayar da kayar baya su mika makamansu da sgiga shirinmu na samar da zaman lafiya.

"Yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatina ta fara ta samu nasarori ciki har da kwance damara, da tabbatar da sakin daruruwan mutanen da aka sace, sake budewa kasuwanni da sake dawo da wasu ayyukan tattalin arziki a duk faɗin jihar.

KU KARANTA: Bayan taron addu'a, Sarkin Kano yace 'yan Najeriya da su amince da rigakafin Korona

A wani labarin, Tsohon sakataren yada labarai da shirye-shirye na jam'iyyar PDP, Anietie Okon, ya nuna bacin ransa ga gwamnatin tarayya kan yadda take mu'amala da 'yan ta'adda da 'yan bindiga a kasar, yana mai bayyana martanin gwamnati kan 'yan ta'adda a matsayin mara gamsarwa.

Okon, wani tsohon dan majalisar dattijai daga jihar Akwa ibom, ya yi mamakin dalilin da ya sa Gwamnatin Tarayya ta dirka a kan masu tayar da kayar baya a yankin Kudu Maso Gabas da cikakken karfin soja, a maimakon sanya karfin ta kan ‘yan bindiga, The Gurdian ta ruwaito.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar  Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel