Rundunar sojojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne, in ji Sheikh Gumi

Rundunar sojojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne, in ji Sheikh Gumi

- Shahararren malamin addinin Islama Gumi, ya bayyana maunfarsa na cewa akwai bara-gurbi a sojoji

- Malamin yace, sojojin basu fahimci asalin sakon da yake isarwa a cikin kalaman nasa ba

- Malamin, yace yana magana kan sojoji da suka gurbata kasar a baya tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi karin haske kan kalaman da ya yi a baya, bayan da rundunar sojin Najeriya ta gargade shi kan abin da ta ce kalaman da ka iya tada husuma a kasa.

Sai dai, Sheikh Gumi ya ce rundunar sojojin ba ta fahimci kalaman shi ba ne kwata-kwata.

Ya ce kalaman da ya yi na cewa akwai bara-gurbi masu mugun hali da nufi a cikin rundunar, yana nufin a tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015 ne.

KU KARANTA: Kwadago zata fara zanga-zangar baji-ba-gani kan batun mafi karancin albashi

Rundunar sojojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne, in ji Sheikh Gumi
Rundunar sojojin Najeriya ba ta fahimci kalamaina ba ne, in ji Sheikh Gumi Hoto: The Nation
Asali: UGC

"Da nake magana kan matsalolin da ke rundunar sojin Najeriya, ina nufin lokacin shekarun 2010 zuwa 2015 ne, lokacin da wasu mutane da ke rike da madafun iko a rundunar suka bari mugayen abubuwa su ka yi ta faruwa."

"A lokacin ne aka rika sa abubuwan fashewa har muka rasa wani babban Janar din soja. Ni kaina na tsallake rijiya da baya da aka sa min abin fashewa," ya shaida wa BBC.

Sheikh Gumi ya bayyana wa BBC cewa yana da kyakkyawar fahimta da rundunar sojin Najeriya kuma babu abin da ya sauya.

KU KARANTA: Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP

A wani labarin daban, Shahrarren Malamin Addini mai kokarin samar da zaman lafiya ta hanyar ayi sulhu da tsagerun yan bindiga, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi wa hukumar Sojin Najeriya martani.

Gumi ya yi raddi ne bayan hukumar Sojin ta gargadesa a wani jawabi da ta saki kan maganar da yayi dake zargin Sojoji Kirista da kashe Fulani masu rike makamai. Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook.

A ranar Litinin, Rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen fiaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel