Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP

Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP

- Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta shaidawa 'yan Najeriya cewa, ta shirya don karbar mulki a 2023

- Jam'iyyar ta yi ikirarin cewa, za ta tsayar dan takara na gari da zai kawo karshen tashin tashina a kasar

- Hakazalika, jam'iyyar ta bayyana cewa, 'yan Najeriya na bukatar ta domin magance rashin tsaron kasar

Jam’iyyar PDP ta bayyana kwarin gwiwar karbar mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki a shekarar 2023.

Sakataren yada labaran ta na kasa, Kola Ologbondiyan, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise wanda The Nation ta nakalto.

Ya ce: “A shiyya daya daga cikin shida, muna da dan takarar mulkin da ke haifar da rashin jituwa wanda tuni kwamitin sulhu karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki ta sasanta.

KU KARANTA: Yanzu nan: Gwamna Dapo Abiodun ya zama gwamna na faro da ya fara yin rigakafin Korona

Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP
Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP Hoto: The Sun News
Asali: UGC

“Jam’iyyarmu fata ce ta 'yan Najeriya kamar yadda muke magana a yau. Ayyukan ta'addanci, tada zaune tsaye, satar mutane sun mamaye al'ummarmu...Hakan ya nuna karara cewa 'yan Najeriya suna tunanin wanda zai ceci al'ummarmu.

"PDP ta shirya tsaf domin karbar ragamar shugabanci ta hanyar akwatin zabe a 2023."

Ya lura cewa rikicin da ke tsakanin Tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose da Gwamnan Oyo Seyi Makinde kwamitin da Saraki ke jagoranta ya warware shi.

Ya ce Saraki ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP na Ogun da na Ekiti kuma ana tattaunawa iri-iri a jam’iyyar.

Ya lura cewa karuwar rashin tsaro, 'yan bindiga da sace dalibai ya nuna akwai bukatar 'yan amshin shatan kasashen waje.

KU KARANTA: Wani sanata ya caccaki gwamnatin Buhari da sakewa 'yan bindiga fuska

A wani labarin daban, Tsohon shugaban majalisar dattawan Najariya Bukola Saraki ya ce, bai kamata a barwa jam'iyyar APC mai mulki matsalar Najeriya ba ita kadai ta shawo kansu ba, BBC Hausa ta rwaito.

Saraki wanda shi ne ke jan ragamar kwamitin sasantawa na jam'iyyar PDP, ya nuna cewa akwai bukatar hada hannu da 'yan hamayya domin lalubo mafitar da za a yi maganin matsalolin Najeriya baki daya, musammam a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel