Yanzun nan: Gwamna Dapo Abiodun ya zama gwamna na farko da ya fara yin rigakafin Korona
- Gwamnan jihar Ogun ya yi allurar rigakafin Korona a yau Talata da tsakar rana a Abeokuta
- Gwamnan shine na farko cikin jerin gwamnoni a Najeriya da ya fara yin alllurar ta Korona
- Hukumar NPHCDA tana ci gaba da jawo hankalin 'yan Najeriya kan su mika kansu ga yin allurar
Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun, ya yi alurar rigakafin Korona na AstraZeneca - gwamna na farko a kasar da ya yi hakan, The Cable ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya na jihar, Tomi Coker, ne ta yi wa Abiodun wannan allurar a ranar Talata, a Abeokuta.
An yi wa gwamnan rigakafin ne tare da Noimot Salako-Oyedele, mataimakin gwamnan, da sauran ma'aikatan lafiya na gaba a jihar.
Gwamnan jihar ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, "Na yi kashi na farko na allurar Astra-Zeneca ta Korona da aka kawo jiya Abeokuta. Mataimakin na, Engr. Noimot Salako-Oyedele da ma'aikatan lafiya na gaba suma an yi musu nasu."
KU KARANTA: Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP
ranar Litinin, gwamnatin jihar ta karbi alluran rigakafin Korona na AstraZeneca guda 50,000.
Hukumar bunkasa kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA) ta ce ta fara rarraba maganin ga jihohin kasar.
Najeriya ta fara allurar rigakafin Korona tare da farawa da ma’aikatan lafiya na gaba a Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kawo yanzu, baya ga wasu ma’aikatan lafiya na gaba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, da wasu jami’an gwamnati sun yi allurar rigakafin.
NPHCDA ta roki 'yan Najeriya da suyi rajista ta yanar gizo domin yin allurar ta Korona.
KU KARANTA: Mun shirya tsaf don karbar ragamar mulkin Najeriya a zaben 2023, jam'iyyar PDP
A wani labarin daban, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha ya ce ba wanda zai tsira daga kamuwa da cutar Korona har sai an yiwa kowa rigakafi, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Mutspaha ya fadi haka ne a ranar Juma'a yayin gabatar da alluran rigakafin COVID-19 a Asibitin Kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.
“A gare mu a Najeriya da kuma kasashen duniya gaba daya, darussan da za a dauka daga wannan rashin nuna wariyar ta kwayar suna da yawa. Sun hada da gaskiyar cewa dole ne mu kusanci yin allurar rigakafin tare da hadin kai ga manufar.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng