Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da na Buhari, Inji gwamnatin tarayya

Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da na Buhari, Inji gwamnatin tarayya

- Gwamnatin Najeriya tace allurar da za'a yima ƴan Najeriya irisu ɗaya da wacce akayi ma shugaban ƙasa da mataimakinsa

- Shugaban hukumar lafiya ta ƙasa ya ce shirye-shirye sunyi nisa wajen rarraba rigakafin zuwa jihohi.

- Za'a ƙaddamar da fara rigakafin a matakin jihohi ranar 10 ga watan maris

Gwamnatin tarayya ta ce allurar rigakafin da za'a yiwa 'yan Najeriya iri ɗaya ce da wanda akayima shugaban ƙasa manjo janar Muhammadu Buhari.

Shugaban hukumar lafiya, Dr. Faisal Shu'aib ne ya faɗi hakan yayin taron kwamitin yaƙi da cutar corona a Abuja, Punch ta ruwaito.

Najeriya ta ƙaddamar da fara rigakafin a ranar Juma'a. Sannan a ranar Asabar aka tsirawa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin kuma annuna a kafar talabishin kai tsaye.

KARANTA ANAN: Tsohon shugaban kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu

Duk ɗan Najeriya da yakeson a masa rigakafin ya je shafin hukumar lafiya (NPHCDA) ya yi rejista.

Yayin da yake jawabi ranar litinin, Dr. Faisal yace: "Abinda kaddamarwar ke nufi shine anfara rigakafin corona a Najeriya.

Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da wadda akayi ma Buhari, Inji gwamnatin tarayya
Za'a yiwa 'yan Najeriya allurar rigakafi iri ɗaya da wadda akayi ma Buhari, Inji gwamnatin tarayya Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

Kuma yana da matuƙar amfani ganin yadda akayiwa shugaban ƙasa da mataimakinsa rigakafin ta Astrazeneca daga cikin 3.98 miliyan da suka iso."

"Babu wani banbanci tsakanin allurar da akayi ma shugaban ƙasa da kuma wacce za'a yima 'yan Najeriyan da suka cancanta," a cewar Faisal.

"Munyi imani cewa yin rigakafin a bainar jama'a zai gina yarda, ƙarfin gwuiwa da kuma karsashi a zuƙatan jama'a don su amince ayi musu," inji Dr. Faisal.

Ya kuma ƙara da cewa kamar yadda sanarwa ta gabata a baya akan shirye-shiryen fara allurar, kwamitin yaƙi da cutar tare da hukumar lafiya sun shirya bada horo ga jami'an lafiya.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gina kowace kilomita ɗaya ta hanyar Abuja-Kano

An fara bada horon ne tun daga matakin ƙasa, dana jiha, da na kananan hukumomi.

Shugaban NPHCDA ga ƙara da cewa anfara rarraba allurar rigakafin zuwa jihohi a yau, kuma ana sa ran zuwa gobe za'a kammala.

Mafi yawancin gwamnoni sun amince su ƙaddamar da fara rigakafin a ranar 10 ga watan maris.

A wani labarin kuma Rundunar soji tayi martani ga Shahararren Malaminnan Sheikh Gumi akan tsokacinsa kan sojoji Kiristoci

Ta tabbatar da cewa dakarunta basu yi wa wata kabila ko addini aiki, don haka ya guji alakanta su da hakan

Rundunar ta yi martani a kan ikirarinsa na cewa sojojin da ba Musulmi bane ke kashe 'yan bindiga

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Source: Legit

Online view pixel