Rundunar soji tayi martani ga Gumi akan tsokacinsa kan sojoji Kiristoci
- Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta aikewa Sheikh Ahmed Gumi jan kunne da kakkausar murya
- Rundunar ta yi martani a kan ikirarinsa na cewa sojojin da ba Musulmi bane ke kashe 'yan bindiga
- Ta tabbatar da cewa dakarunta basu yi wa wata kabila ko addini aiki, don haka ya guji alakanta su da hakan
Rundunar sojin Najeriya ta ja kunnen fiaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci.
Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Birgediya janar Mohammed Yerima a wata takarda da ya fitar ya ja kunne malamin da ya kiyaye yadda zai dinga kwatanta rundunar sojin.
Ya ce: "Hankalin rundunar sojin Najeriya ta kai kan wani bidiyo da ke nuna fitaccen malami Sheikh Ahmed Gumi yana zargin sojojin da ba musulmi ba da harar 'yan bindiga.
KU KARANTA: Da duminsa: Gagararren makashin makiyayi, Iskilu Wakili ya shiga hannun hukuma a Oyo
"A wannan bidiyon, an ga malamin yana sanar da 'yan bindiga cewa sojojin da ke kai musu hari yawanci ba musulmi bane. Ya kara da bayyana cewa su sani, sojoji sun rabu, musulmi da wadanda ba musulmi ba.
"Yayin da rundunar bata son hada zantuka da Shehin malamin, akwai matukar amfani a san cewa rundunar bata tura dakarunta aikin kabilanci ko addini.
“A don haka take kira ga Sheikh Gumi da sauran masu fadin ra'ayoyinsu da su gujewa saka rundunar cikin irin wadannan lamurran domin gujewar zubewar mutuncin daya daga cikin mafi nagartar ma'aikatu a kasar nan."
KU KARANTA: Hotunan auren matashin da yayi wuff da tsulan-tsulan 'yammata 2 a rana daya
A wani labari na daban, ma'aikatar ilimi ta jihar Kwara ta soke hukuncinta na sake bude wasu makarantu 10 na jihar inda aka yi rikicin saka hijab.
Kamar yadda babbar sakatariyar ma'aikatar, Kemi Adeosun ta tabbatar, da farko an bukaci makarantun su bude a ranar Litinin amma an soke hakan.
Ta ce wannan hukuncin an yanke shi ne saboda wasu dalilan tsaro, Premium Times ta wallafa.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng