Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gina kowace kilomita ɗaya ta hanyar Abuja-Kano

Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gina kowace kilomita ɗaya ta hanyar Abuja-Kano

- Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince ta fidda zunzurutun kuɗin da suka kai 2.23 biliyan don sake gina kilomita ɗaya ta hanya

- Gwamnatin ta amince da zunzurutun kuɗaɗe da suka kai 797.23 biliyan don sake gina hanyar Abuja zuwa Zaria zuwa Kano

- Ana ganin waɗannan kuɗaɗe sunyi yawa, inda aka hasaso cewa ana bada aiki makamancin wannan ga wasu kamfanoni a kan 90 biliyan

Gwamnatin Najeriya ƙarkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta amince da fitar da maƙudan kuɗaɗe don sake gina hanyar data taso daga Abuja zuwa Kano.

KARANTA ANAN: Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta koka kan yawan sace mata 'yan makaranta

A rahoton da jaridar PM News ta ruwaito, Gwamnatin ta amince ta fidda 797.23 biliyan don sake gina hanyar.

Hanyar data taso daga Abuja ta ratsa ta Kaduna da Zariya ta isa babban birnin jihar Kano ce aka fiddama waɗannan kuɗaɗe.

Hanyar da keda tsawon kilomita 357 zata laƙume 2.23 biliyan akan kowacce kilomita ɗaya.

KARANTA ANAN: Tsohon shugaban kwalejin ilimi (FCE) ta Zariya, Dr. Ango A. Ladan ya rasu

Da farko dai an fidda ma hanyar 155 biliyan a shekarar data gabata, aka bawa kamfanin 'Julius Berger' amma aikin yaƙi gamuwa.

Kuɗi Masu Gidan Rana, Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gida kilomita ɗaya ta hanya
Kuɗi Masu Gidan Rana, Gwamnatin Buhari ta amince ta fidda 2.23 biliyan don sake gida kilomita ɗaya ta hanya Hoto: @NGRpresident
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar wakilai ta kasa, Kabir Sulaiman, yace an bada wasu ayyukan hanya da suke dai-dai da wannan tsawon ga wasu kamfanoni a kan 90 Biliyan.

A wani labarin kuma Hukumsar dake shirya jarabawar share fagen shiga jami'a a Najeria (JAMB) tace ta tara zunzurutun kuɗaɗe da suka kai 400 biliyana shekara ɗaya

Mai kula da aje bayanan ɗalibai na hukumar, Prof. Is-haq Oloyede, ya ce a shekararsa ta farko a wannan ofishin ya tara waɗannan kuɗaɗen masu yawa.

Shugaban ya yi wannan jawabi ne yayin wani taron ƙara wa juna sani da NYSC ta shiryawa makarantun gaba da sakandire da kuma wasu masu ruwa da tsaki.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262