Korarren hadimin Ganduje, Yakasai a karshe dai yayi magana
- Tsohon hadimin gwamna Ganduje kan harkokin yada labarai, Yakasai, ya ce ya bar gwamnatin da miliyoyin alheri
- An ruwaito cewa an kori tsohon hadimin yada labaran ne saboda sukar Gwamnatin Buhari
- Yayin da gwamnan jihar Kano ya kori Yakasai, jami'an 'yan sanda na sirri na DSS sun kama shi
Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai ba gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya bayyana korar tasa a matsayin "fita mai mutunci".
Gwamna Ganduje ya kori Yakasai daga aiki ne saboda wani jawabi da ya yi na kira mai matukar muhimmanci ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da korarsa a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu.
KU KARANTA: Wata sabuwa: Sowore a kotu tare da wani mai tsaron da ba a saba gani ba
Legit.ng ta lura cewa korar Yakasai ta biyo bayan wani bayani ne a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu, inda ya caccaki gwamnati mai ci kan sace wasu ‘yan mata 'yan makaranta a jihar Zamfara.
Kwanaki bayan sallamar, tsohon hadimin a ranar Litinin, 8 ga Maris, ya ce ya bar gwamnati da kyakkyawar niyya fiye da wacce ya samu lokacin da aka shigeta.
Ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa:
"Bayan shekara 5 a cikin Gwamnati, farin cikin da na samu bayan na bar Gwamnati, ya ninka wanda na samu lokacin da na shiga sau miliyan.
"Wannan hakika hanyar fita mai martaba ce, wacce ba kasafai ake yin ta ba a Najeriya. Wannan hakika aikin Allah ne kuma ina mai gode masa saboda ni'imominsa marasa iyaka"
KU KARANTA: Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta koka kan yawan sace mata 'yan makaranta
A wani labarin, Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce kame Malam Salihu Tanko-Yakassai, hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya biyo bayan batutuwan da suka wuce na bayyana ra'ayi a kafafen sada zumunta.
Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Dakta Peter Afunanya, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, Vanguard News ta ruwaito.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng