Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona

Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona

- Fadar shugaban kasa ta shaidawa 'yan Najeriya cewa rigakafin Korona na da tasiri mai kyau

- Fadar ta kuma bayyana cewa, Buhari bai ji wani wahala ba bayan yin allurar rigakain ta Korona

- Hazalika shugaban kasa ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi kokarin amincewa da allurar rigakafin

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari bai sha wata wahala ba bayan yin allurar AstraZeneca ta Korona, TheCable ta ruwaito.

Buhari da Osinbajo sun yi allurar rigakafin a fadar shugaban kasa dake Abuja, ranar Asabar.

A wani yunkuri na kawar da fargabar ‘yan Najeriya, Shehu ya tabbatarwa 'yan kasar amincin allurar rigakafin, yana mai cewa shugaban “ya ji garau ya ci gaba da harkokinsa” bayan an yi masa rigakafin.

Ya kara da cewa idan har akwai illoli, to fadar shugaban kasa ba zata yi rufa-rufa akai ba.

KU KARANTA: Gwamnati bata isa ta hana kiwo a fili ba, in ji Miyetti Allah Kautal Houre

Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona
Fadar Shugaban Kasa: Buhari bai jikkata ba bayan yin rigakafin Korona Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

"A cikin amsa ga tambayoyin manema labarai, ina so in tabbatar wa dukkan 'yan kasa, kuma in kawar da tsoro da rashin fahimta game da lafiyar allurar rigakafin da aka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa, SAN a safiyar yau," in ji Shehu a cikin sanarwa.

“Bayan ya sami jab din sa, Shugaban kasan ya sami nutsuwa ya kuma ci gaba da aikin sa. Idan akwai wasu illoli da suka biyo baya, za mu kasance a buɗe game da hakan amma har yanzu babu wani abu na illa, mai tsanani ko taushi ga Shugaban. Yana ci gaba kamar yadda ya saba.

"Muna fatan wannan zai taimaka wajen isar da sako mai karfi a tsakanin mutane, musamman wadanda ke kokawa game da inganci da amincin allurar."

Bayan yin allurar, Buhari ya bayyana shawarar da ya yanke na yin allurar a bainar jama'a a matsayin "nuna jagoranci da imani kan aminci da ingancin alluran".

Shugaban ya ba da shawarar allurar ga duk wani dan Najeriya da ya cancanta, yana mai cewa tana da matukar kariya daga kwayar cutar.

"Na yi allurata ta farko kuma ina so in ja hankalin duk 'yan Najeriya da suka cancanta, su yi hakan domin a kare mu daga kwayar, cutar" in ji shi.

KU KARANTA: Hayakin Janareta ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daliban jami'a 2

A wani labarin, Shugaban kwamitin yaki da kwayar cutar korona a Najeriya (PTF), Boss Mustapha, ya ce nan gaba katin shaidar yi wa mutum allurar rigakafin cutar zai zama wajibi ga matafiya kasashen waje, BBC Hausa ta ruwaito.

Mustapha wanda kuma shi ne sakataren Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban Kasa a yau Asabar jim kadan bayan an yi wa shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo allurar rigakafin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel