Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta koka kan yawan sace mata 'yan makaranta

Da dumi-dumi: Aisha Buhari ta koka kan yawan sace mata 'yan makaranta

- Uwargidan shugaban kasar Najeriya ta bayyana rashin jin dadinta da yawan sace-sace a kasar

- Ta koka kan yadda ake sace 'yan mata a makarantu wanda hakan a cewarta barazanace ga ci gaban mata

- Ta bukaci da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro da su mai da hankali kan gyara lamarin rashin tsaro a arewa

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta koka kan yadda ake ci gaba da sace mata da ‘yan mata da 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya ke yi, musamman a arewa.

Aisha a cikin wata sanarwa a yayin bikin ranar mata ta duniya da aka wallafa a shafinta na Twitter mai suna @aishambuhari, ta ce: "A matsayina na uwa, ina jin bakin ciki da radadi ga wadanda abin ya shafa da iyalansu".

KU KARANTA: Da duminsa: An yiwa Marwa, Gambari da Garba Shehu rigakafin Korona

"Ni ban san tasirin da wadannan sace-sacen za su iya yi ba wajen juya akalar nasarorin da muka samu zuwa yanzu, musamman ta fuskar ilimin 'ya-ya mata da kuma auren wuri."

Ta kuma yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su yi amfani da matakan da suke da shi wajen kawo karshen sace-sacen mutane.

Yayin da take yabawa kokarin mata da 'yan mata a yakin da ake yi da Korona, ta lura cewa wannan annoba ta yi matukar tasiri ga mata, ta hargitsa ilimi, sana'oi da kuma yawaitar rikice-rikicen cikin gida.

KU KARANTA: Jihar Katsina ta gurfanar da Dr Mahadi Shehu a gaban kotu da zargin batanci

A wani labarin, Shugaba/wadda ta assasa kungiyar mata ta Aspire, Barista Zainab Marwa-Abubakar, ta ce akwai yiwuwar mace ta gaji Shugaba Muhammadu Buhari, Daily Trust ta ruwaito.

Ta fadi haka ne a ranar Lahadi a taron masu ruwa da tsaki na mata a Abuja. Shirin na daga cikin ayyukan bikin ranar mata ta duniya ta bana.

“Yayin da 2023 ke gabatowa, na yi imanin cewa mata za su ɗauki haƙƙinsu, a matsayinsu na shugabanni, masu tsara manufofi da masu yanke shawara a cikin wannan rawar neman mulki.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel