Yahaya Bello zai magance matsalar tsaro a Najeriya kamar yadda ya yi Kogi idan...
- Wata kungiyar gangamin takarar Yahaya Bello ta bayyana kwarewarsa a yakar rashin tsaro
- Kungiyar tace Yahaya ne ke da sinadarin magance matsalar tsaro a kasar kamar yadda aya yi Kogi
-Hakazalika kungiyaerta yabawa shugaba Buhari a kokarinsa, amma ta bukacin shugaban ya kara zage damtse
Wata kungiyar siyasa dake goyon bayan Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ta ce shi (Bello) zai magance matsalar rashin tsaro a Najeriya, tare da yin amfani da dabarun da ya yi amfani da su wajen kiyaye jihar sa lafiya, The Nation ta ruwaito.
Kungiyar ta bayyana gwamnan a matsayin wanda yafi kowa cancanta ya maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Kungiyar ta lura da fitowar Gwamnan zai kawo karshen matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar nan cewa zai yi amfani da dabarun da ya bi a Jihar Kogi don magance matsalolin tsaro na kasar.
KU KARANTA: Sojoji sun bindige wasu 'yan bindiga mutum 4 a jihar Kaduna
Kungiyar ta ce Gwamnan ne ya fi dacewa da matsayin idan aka yi la’akari da nasarorin da ya samu a bangaren tsaro na jihar.
Da yake jawabi a wajen bude motar bas mai daukar mutane 18 ta yakin neman zaben Gwamna Yahaya Bello a Abuja, Darakta-Janar na GYB2PYB, Amb. Oladele Nihi yayi nadamar cewa Najeriya a halin yanzu tana fuskantar rashin tsaro da rashin hadin kai.
Duk da cewa matasan sun yaba da kokarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na shawo kan matsalar tsaro, amma sun lura cewa akwai bukatar rubanya kokarin.
Ya ce Gwamna Bello na da abin da ya kamata don magance matsalolin rashin tsaro na kasar duba da yadda ya tunkari matsalar tsaro a jiharsa.
Ya ce: “Mun lura da yadda ya iya shawo kan matsalar rashin tsaro a jihar Kogi musamman ma kasancewar jihar karamar Najeriya ce; tayi iyaka da jihohi tara, gami da babban birnin tarayya.
“Muna godiya ga Shugaba Muhammadu Buhari kan kokarin da yake yi na magance rashin tsaro.
"Amma yanzu muna da karami, matashi wanda ke yin abin al'ajabi dangane da yaki da rashin tsaro a jihar Kogi wanda a shekarar 2023 zai tabbatar da mun kawar da rashin tsaro gaba daya a Najeriya.
“Idan kun lura, kowane lokaci da kowane yanayi yana da nasa maganin. 2015, babbar matsalar kasar kamar yadda aka shaida a lokacin ita ce rashawa da rashin tsaro.
"A yanzu haka babbar matsalar da muke fuskanta ita ce ta rashin tsaro da rashin hadin kai."
DG din ya ce kungiyar za ta tattara matasa miliyan 15 don tallafa wa burin takarar shugaban kasa na Bello a 2023.
KU KARANTA: Kasar Autria ta dakatar da yin rigakafin Korona na AstraZeneca saboda zargin mutuwa
A wani labarin, sohon Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya gargadi Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta tabbatar da cewa satar yaran makaranta bai sake faruwa ba, PM News ra ruwaito.
Atiku ya mayar da martani ne kan sakin 'yan mata 279 na makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, da ke Jangebe, jihar Zamfara a ranar Talata.
Ya ce a matsayinsa na uba, ya yi matukar farin ciki da sakin daliban kuma ya yi wa danginsu murna.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng