Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutune 11 a jihar Kaduna

Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutune 11 a jihar Kaduna

- Rahotanni sun bayyana cewa, an sace wasu mutane 11 a jihar Kaduna da safiyar yau Asabar

- 'Yan bindigan sun kai hari ne unguwar ma'aikatan hukumar kula filayen jirgin sama na Najeriya

- Majiya daga hukumar ta kula da filayen jirgin sama ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai

Wasu 'yan bindiga sun far wa unguwar ma'aikatan hukumar kula da filayen jirgin sama ta Najeriya (FAAN) da ke Jihar Kaduna, inda suka sace mutum 11.

Mai magana da yawun hukumar ta FAAN, Henrietta Yakubu, ta ce 'yan bindigan sun shiga unguwar ce da safiyar yau Asabar, kamar yadda ta shaida wa TheCable.

KU KARANTA: Katin shaidar rigakafin korona zai zama sharaɗin fita daga Najeriya, in jiBoss Mustapha

Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun sace mutune 11 a jihar Kaduna
Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun sace mutune 11 a jihar Kaduna Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: UGC

"Sun dauki ma'aikatanmu kusan tara da kuma iyalansu a unguwar," in ji ta.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan sun shiga unguwar ne bayan sun karya shingen wayar da ya raba filin jirgin da kuma gidajen ma'aikatan. Sai dai ba a samu rahoton rasa rai ba.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa karar harbe-harben da maharan suka yi ya sa wasu sojoji da ke kusa suka mayar musu da martani.

Sai dai daga baya sun gudu da mutanen da suka sata, wadanda jumillarsu ya kai 11.

Lokacin da aka tuntube shi, Mohammed Jalige, kakakin ‘yan sanda a jihar, ya ce zai yi bayani da zaran ya samu cikakken bayani game da harin.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: An yi wa shugaba Buhari rigakafin Korona yanzun nan

A wani labarin, 'Yan bindiga da suka addabi jihar Zamfara galibi ana ganinsu cikin kakin sojoji da muggan makamai.

Gwamnatin Zamfara ta ce an kama wani jami’in Sojan Najeriya da ke ba da alburusai da kakin soja ga ‘yan bindiga a jihar, TheCable ta ruwaito.

A wani taron manema labarai a ranar Juma'a, Bashir Maru, mataimakin shugaban ma'aikata na gwamna Bello Matawalle, gwamnan jihar, ya ce sojoji sun kame jami'in tare da budurwar sa, bayan bayanan sirri da aka samu daga al'umma.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.