Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole

Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole

- Gwamnan jihar Edo ya bayyana babban abinda ke haɗashi da tsohon shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.

- Godwin Obaseki ya ce banda matsalar siyasa bashi da wata damuwa da tsohon gwamnan kuma dukansu suna son cigaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

-Gwamnan yace taron jam'iyarsa ta PDP da aka shirya yi an ɗage sha saboda zaben kananan hukumomi da ake yi a jihar Delta.

Gwamanan jihar Edo, Godwin Obaseki yace bashi da wata matsala data wuce ta siyasa tsakaninshi da tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam'iyar APC Adams Oshiomhole.

Obaseki ya yi watsi da duk wata jita-jita da ake yaɗawa cewa basa jituwa tsakaninsu. Puch ta wallafa.

KARANTA ANAN: Labari mara dadi: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutune 11 a jihar Kaduna

Obaseki da Oshiomhole sun sami matsala tun a watan satunban shekarar da ta gabata lokacin zaben gwamnan jihar, wanda sanadiyyar hakan yasa gwamnan ficewa daga APC ya koma PDP.

Jaridar Puch ta ruwaito gwamnan na cewa, dukkan mu muna da muradin kawo cigaba a jihar da ma ƙasa baki daya.

Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole
Rikicin Siyasa: Gwamnan Edo ya bayyana babban abinda ke haɗa shi da Adams Oshiomhole Hoto: @Governorobaseki
Asali: Twitter

"Bani da wata matsala tsakanina da Oshiomhole, saidai banson tsarin siyasar shi amma bai taɓamun wani abu mara kyau ba a tsakanin mu. Mun haɗu wuri daya da shi ta wajen son cigaban ƙasa da kuma yankin mu," inji gwamnan.

KARANTA ANAN: Da dumi-dumi: An yi wa shugaba Buhari rigakafin Korona yanzun nan

A wani saƙo da mai bawa gwamnan shawara n musamman kan yaɗa labarai, Crusoe Osagie, ya fitar yace gwamnan ya dauke shi a matsayin dan uwa kuma aboki.

Bayan haka, Gwamnan yace an ɗage taron yanki-yanki na jam'iyyar PDP da aka shirya yi ranar Asabar ne saboda zaɓen ƙananan hukumomi da ake yi a jihar Delta.

A wani labarin kuma Sojoji sun sheke 'yan bindiga 4, sun samu miyagun makamai a Katsina

Zakakuran sojin Najeriya sun sheke wasu mutum hudu da ake zargin 'yan bindiga ne karkashin rundunar Operation Hadarin Daji a Katsina.

Sojojin sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a ranar Alhamis a kauyen Marina dake karamar hukumar Safana ta jihar.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta ta instagram @ahmad_y_muhd

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel